Iran Ta Gindaya Sharadin Bude Mashigar Hormuz da Trump Ke Son Ta Yi

Iran Ta Gindaya Sharadin Bude Mashigar Hormuz da Trump Ke Son Ta Yi

  • Iran ta yi magana kan sake bude mashigar Hormuz wadda ta rufe sakamakon yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya
  • Tehran ta bayyana cewa ta cimma matsaya da Oman kan hanyar zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar
  • Hakazalika Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta musanta ikirarin Donald Trump cewa ana tattaunawar cimma yarjejeniya da Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Tehran - Gwamnatin Iran ta bayyana cewa sake bude mashigar Hormuz ga zirga-zirgar jiragen ruwa zai dogara ne kan matakin da Amurka za ta dauka.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya ci gaba da ikirarin cewa Iran na son cimma yarjejeniya da Washington.

Iran ta gindaya sharadi ga Amurka
Shugaba Donald Trump da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai Iran ta musanta hakan, tana mai cewa maimakon haka ta fi mayar da hankali kan cimma matsaya da makwabciyarta Oman game da yadda za a gudanar da zirga-zirga a mashigar, tashar Press tv ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Trump ya fadi zabin Amurka tsakanin sulhu da yaki a Iran

Iran ta yi magana kan yarjejeniya da Oman

Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iran (IRNA) ya ruwaito cewa kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar, Esmaeil Baqaei, ya ce Iran da Oman sun amince kan hanyar da jiragen ruwa za su rika bi a mashigin Hormuz.

Ya ce kasashen biyu na kammala shirye-shiryen fitar da sanarwar hadin gwiwa kan yadda za su gudanar da wannan muhimmiyar hanyar ruwa.

A cewarsa:

"An amince da tsarin hanyar da bangarorin biyu suka tsara, kuma idan wasu bangarori na uku ba su kawo cikas ba, sanarwar hadin gwiwar kasashen biyu na matakin karshe na gyarawa da rubutawa."

Iran ta dora alhakin bude mashigar kan Amurka

Baqaei ya ce ko da an cimma yarjejeniya da Oman, hakan ba yana nufin mashigar za ta kasance cikin aminci ga dukkan jiragen ruwa ba.

Ya ce har yanzu akwai abubuwan da ke hana bude mashigin gaba daya.

A cewarsa:

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Trump ya dauko batun kulla yarjejeniya da Iran bayan barazana

"Dalilan da ke hana mashigin Hormuz kasancewa cikin aminci har yanzu suna nan daga bangaren Amurka, musamman killace tashoshin ruwan Iran da kuma sauran matakan barazana da take dauka kan Iran da muradunta."

Iran ta ce duk wani sassauci wajen bude mashigin zai dogara ne da ko Amurka za ta kawo karshen killace tashoshin ruwan kasar.

Tasirin rikicin mashigar Hormuz

Kafin barkewar yakin, mashigin Hormuz na daukar kusan kashi daya cikin biyar na fitar da danyen mai da iskar LNG na duniya.

Tun bayan rikicin ya barke, farashin makamashi ya rika tashi, lamarin da ya kara matsin tattalin arziki da na siyasa ga Amurka.

Tun bayan barkewar yakin tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila, Iran ta rika sanya ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar tare da yin barazanar daukar mataki kan jiragen da ta ce ba su bi hanyoyin da ta amince da su ba.

Iran ta kafa sharadi ga Amurka
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi Hoto: @Araghchi
Source: Twitter

Trump ya ce Amurka na da makamai

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya dauko batun da ke cewa kasarsa na fuskantar karancin makamai.

Shugaba Trump ya ce Amurka na da dimbin makamai kuma ana kera wasu yayin da ya yi watsi da batun cea wasu muhimman makamai sun kusa karewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng