Gwamna Abba Ya Shiga Alhini da Wani Babban Malamin BUK, Dr. Labaran Ya Rasu a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar babban malami a jami'ar BUK, Dr.Musa Adamu Labaran
- Malamin ya rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya ranar Litinin da ta gabata, 25 ga watan Mayu, 2026
- Abba Gida-Gida ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa tare da sanya shi a Aljannatul Firdausi, Ya kuma ba iyalansa hakuri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya bayyana alhini matuƙa kan rasuwar fitaccen masanin sadarwa, Dr.Musa Adamu Labaran.
Marigayin wanda ke aiki a Tsangayar Sadarwa ta Jami'ar Bayero da ke Kano (BUK) ya riga mu gidan gaskiya ne a jiya Litinin bayan gajeruwar rashin lafiya.

Source: Facebook
Babban malamin jami'ar BUK ya rasu
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kafin rasuwarsa, Dr. Labaran babban malami ne a BUK kuma Mataimakin Shugaban Sashen Sadarwa, Sashen Bayanai da Nazarin Kafafen Yaɗa Labarai na jami'ar.
Ya rasu a Kano da sanyin safiyar Litinin bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya, a cewar Shugaban Sashensa, Farfesa Nura Ibrahim.
Farfesa Ibrahim ya ce marigayin malamin ya yi korafin rashin lafiya a ranar Juma'a sannan daga baya ya ziyarci asibiti don neman magani.
"Bayan likita ya duba shi ya ba shi magani, ya ji sauki kuma ya ci gaba da ayyukansa, sai kawai muka farka da labarin mutuwarsa. Ma'aikaci ne mai himma. Muna addu'ar Allah ya gafarta masa," in ji shi.
Gwamna Abba ya yi ta'aziyyar Dr. Labaran
A cikin saƙon ta’aziyyar da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature, ya wallafa a Facebook, Abba ya bayyana rasuwar Dr Labaran a matsayin babban rashi ga fannin ilimi, harkar yaɗa labarai da kuma al’umma baki ɗaya.
Ya ce marigayin ƙwararren malami ne kuma masani wanda gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa karatun sadarwa, binciken harkokin yaɗa labarai za ta ci gaba da kasancewa mai amfani na dogon lokaci.
Abba Kabir ya ƙara da cewa Dr Labaran ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa, bincike da horas da ɗalibai da ƙwararru da dama, inda ya bar tarihi na ƙwarewa, gaskiya da hidima ga bil’adama.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta ba da hutun babbar Sallah, ta aika sako ga musulmin Najeriya

Source: Facebook
Abba ya yi wa marigayin addu'a
A cewar gwamnan, rasuwar tasa ta haifar da babban giɓi a fannin ilimi da sadarwa saboda jajircewarsa wajen yaɗa ilimi.
Gwamna Abba ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa tare da sanya shi a Aljannatul Firdausi.
Haka kuma ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, al’ummar jami’a, ‘yan jarida, abokai da sauran masu alaƙa da shi a wannan lokaci na jimami.
Gwamna Abba ya ba da goron Allah
A wani labarin, kun ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da bayar da tallafin Babbar Sallah na N20,000 ga kowane ma’aikatan gwamnati a jihar Kano.
Gwamnatin Kano ta ce tallafin zai shafi ma’aikatan da ke aikigeeeggccgcc a ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati na jihar da kuma ma’aikatan ƙananan hukumomi.
Matakin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan gwamnati ta biya albashin watan Mayu, 2026 ga ma’aikatan jihar da na ƙananan hukumomi a Kano.
Asali: Legit.ng
