2027: Jam'iyyar ADC Ta Amince Mutum 3 Su Nemi Takarar Shugaban Kasa a Najeriya
- ADC ta amince masu neman takarar shugaban kasa uku su kece raini a zaben fitar da gwanin da za ta shirya ranar Litinin mai zuwa
- Mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ya tabbatar da cewa an tantance Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi da Mohammed Hayatu-Deen
- Haka zalika ADC ta tantance masu neman takarar gwamna 80, ciki har da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami (SAN)
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jam'iyyar adawa ta ADC ta tantance tare da amincewa da masu neman takarar shugaban ƙasa uku na jam’iyyar domin shiga zaɓen fitar da gwanin da za a gudanar ranar Litinin.
Duka 'yan siyasar uku sun bayyana gaban kwamitin tantance masu neman takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jagorancin Liyel Imoke.

Source: Twitter
ADC ta tantance Atiku da mutum 2

Kara karanta wannan
2027: Kakakin majalisar Kwara ya raba gardama a zaben fitar da dan takarar gwamnan APC
Punch ta ce wadanda ADC ta tantance sun haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar; tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi; da fitaccen masanin tattalin arziki, Mohammed Hayatu-Deen.
Sakataren yaɗa labarai na ADC ta kasa, Bolaji Abdullahi, wanda ya bayyana hakan ranar Asabar, ya ce an kuma tantance masu neman takarar gwamna 80.
Ya ƙara da cewa an amince da ‘yan takarar sanata 109 da kuma ‘yan takarar kujerun majalisar wakilai 513 bayan sun bayyana gaban kwamitocin tantancewa domin shiga zaɓen ftar da gwani na jam’iyyar.
Fitattun masu neman takarar gwamna
Daga cikin masu neman takarar gwamna da suka bayyana gaban kwamitin akwai tsohon gwamnan Adamawa, Mohammed Umaru Jibrilla; da tsohon ministan shari’a kuma Antoni Janar na tarayya, Abubakar Malami.
Sauran jiga-jigan da ke namen tikitin takarar gwamna a ADC sune Great Ogboru; Mohamed Onawo; Gbadebo Rhodes-Vivour; da wasu fitattun ‘yan siyasa daga jihohi daban-daban.
Bolaji Abdullahi ya ce jam’iyyar ADC za ta gudanar da zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa ranar Litinin 25 ga Mayu, 2026.
ADC ta shirya zaben fitar da gwani
A wata hira da ya yi da jaridar Nigerian Tribune, ya bayyana cewa an riga an tura jami’an zaɓe zuwa jihohin ƙasar nan domin tabbatar da gudanar da zaɓe cikin nasara.
Ya nuna fatan cewa zaɓen zai gudana cikin lumana, adalci da gaskiya, yana mai cewa dukkan ‘yan takarar uku sun amince za su karɓi sakamakon zaɓen.

Source: Facebook
Mai magana da yawun ADC ya ce an gudanar da zabukan cikin nasara ba tare da wata matsala ba, kamar yadda Daily Post ta kawo.
A cewarsa:
“Wannan shi ne karo na farko da ADC ke gudanar da irin wannan babban tsari. Don haka ana iya samun ƙananan matsaloli nan da can, amma muna da kwarin gwiwar cewa gaba ɗaya zaɓen zai yi nasara."
Amaechi zai zama abokin takarar Atiku?
A baya, kun ji cewa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya ce bai sayi fom domin ya zama mataimakin shugaban kasa ba a zaben 2027.
Amaechi, tsohon gwamnan jihar Ribas ya nuna rashin jin dadinsa kan rade-radin cewa zai iya zama abokin takarar Atiku Abubakar a jam’iyyar ADC.
Kalaman nasa sun jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu ‘yan Najeriya suka goyi bayansa, yayin da wasu suka soki yadda ya mayar da martani.
Asali: Legit.ng
