"Ina cikin Hadari": Tsohon Shugaban NHIS Ya Mika Korafi kan Kwankwaso ga 'Yan Sanda

"Ina cikin Hadari": Tsohon Shugaban NHIS Ya Mika Korafi kan Kwankwaso ga 'Yan Sanda

  • Tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf ya nuna rashin gamsuwa da wasu kalamai da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi
  • Farfesa Usman Yusuf ya yi zargin cewa Kwankwaso ya yi kalaman da za su tunzura jama'a a kansa kuma hakan ya jefa rayuwarsa a hadari
  • Tsohon shugaban na hukumar NHIS ya bukaci 'yan sanda su gayyaci Kwankwso domon su yi masa tambayoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya shigar da ƙorafi kan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Farfesa Usman Yusuf ya shigar da korafin ne kan Kwankwaso gaban rundunar ’yan sandan Najeriya da hukumar tsaron farin kaya (DSS) bisa zargin kalaman tunzura jama'a da tsohon gwamnan ya yi a kansa.

An kai korafin Kwankwaso gaban 'yan sanda
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Farfesa Usman Yusuf Hoto: Hon. Saifullahi Hassan, EFCC Nigeria
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa takardar ƙorafin na dauke da kwanan watan ranar, 22 ga watan Mayu, 2026.

Kara karanta wannan

"Ku zabe ni": Amaechi ya bayyana shirinsa ga 'yan Najeriya idan ya zama shugaban kasa

Meyasa aka shigar da korafi kan Kwankwaso?

Farfesa Usman Yusuf ya zargi Kwankwaso da yin kalamai masu tada hankali a lokacin wani jawabi ga jama'a, biyo bayan kalaman da shi (Yusuf) ya yi a kafafen yaɗa labarai kwanan nan game da haɗin gwiwar siyasa da kuma batutuwan siyasar shiyya.

A cewar tsohon shugaban na NHIS, ko da yake Kwankwaso bai ambaci sunansa kai-tsaye ba a lokacin jawabin, siffar da ya yi amfani da ita ta fito da shi fili ga magoya baya da mabiya da ke da masaniya kan batutuwan da ake tattaunawa akai.

Usman Yusuf ya yi zargin cewa Kwankwaso ya yi kira ga mambobin kungiyar Kwankwasiyya da ƙungiyoyin matasan siyasa da ke tafi da su da su "wargaza" mutumin da ake magana a kai ta hanyar amfani da kalmar Hausa ta "pata-pata".

Farfesa Usman Yusuf ya yi gargadi

Ya yi gargaɗin cewa idan aka yi duba da yanayin siyasa da ake ciki a yanzu da kuma tarihin tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa a wasu sassan ƙasar, bai kamata a ɗauki kalaman da wasa ba, shafin symfoninews ya kawo rahoton.

Kara karanta wannan

"Kada a zalunci El Rufa'i": Tsohon jigon APC ya roki dattawan Arewa su saka baki

“Ina ɗaukar waɗannan kalamai a matsayin masu haɗari, masu tunzura jama'a, da kuma waɗanda za su iya jefa lafiyata da ta iyalina cikin haɗari."

- Farfesa Usman Yusuf

Usman Yusuf ya shigar da korafi kan Kwankwaso
Tsohon shugaban hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf Hoto: @Somto_Chukwu
Source: Twitter

Wace bukata ya nema?

Ƙorafin ya buƙaci hukumomin tsaro da su rubuta ƙorafin a hukumance, su gayyaci Kwankwaso domin yi masa tambayoyi, sannan su ɗauki matakan kariya domin kauce wa duk wata barazana ga Usman Yusuf da sauran abokansa.

Haka zalika, Usman Yusuf ya jaddada buƙatar kare haƙƙoƙin ƴan ƙasa na bayyana ra'ayoyinsu cikin ƴanci da kuma shiga cikin tattaunawar ƙasa ba tare da fargabar tsoratarwa ko hare-hare masu nasaba da siyasa ba.

Bugu da ƙari, ya yi kira ga shugabannin siyasa a duk faɗin jam'iyyu daban-daban da su kiyaye kalaman da suke yi a gaban jama'a kuma su guji kalaman da ke da ikon tunzura magoya baya ko gurgunta zaman lafiyar al'umma.

Kwankwaso ya magantu kan yi wa Tinubu aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi martani kan zargin cewa yana yi wa Shugaba Bola Tinubu aiki don zaben 2027.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kwankwaso ya yi martani kan zargin yana yi wa Tinubu aiki

Rabiu Kwankwaso ya yi watsi da iƙirarin da ke nuna cewa yana aiki ne domin muradin Shugaba Bola Tinubu gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Tsohon dan takarar shugaban kasar a zaben 2023 ya ƙaryata zargin, inda ya bayyana cewa wawayen mutane kawai za su yarda da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng