Manyan Labarai A Yau
Wasu jiga-jigan PDP biyu a jihar Gombe sun yi murabus daga jam’iyyar gabanin zaben 2027, amma ba su bayyana dalilan ficewarsu ba daga jam'iyyar mai adawa ba.
Trump ya ce wannan ce dama ta ƙarshe da Iran za ta amince da yarjejeniya, yayin da ya jaddada cewa ba zai amince Tehran ta karɓi kuɗin wucewa ta mashigin Hormuz ba.
Hukumar Hisbah ta Yobe ta dakatar da bikin 'Colour Festival' a Damaturu, yayin da Hisbah ta Kano ta kama wani ɗan TikTok kan zargin ƙarfafa zina.
Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana yin kuskure kan zaben 2027.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce Iran na da zabin kulla yarjejeniya ko mika wuya gaba daya, yayin da Tehran ta musanta cewa ana tattaunawa.
Jam'iyyar APM reshen jihar Legas ta bayyana cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ne ya kamata 'yan adawa su tsaida a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Bishop David Oyedepo ya ce gwamnatin tarayya ba ta yi isasshen kokari wajen dakile kashe-kashe a Najeriya ba, yana mai cewa zai yi addu'a a kan masu aikata laifukan.
Ministan ayyuka, David Nweze Umahi, ya bayyana sakon da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba shi yayin da ake kiran ya tsige shi daga mukaminsa.
Iran ta ce ba ta shiga wata tattaunawa da Amurka ba, duk da cewa Donald Trump ya ce za a fara tattaunawa domin kawo karshen yakin da ya shafe watanni shida.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari