Wata Sabuwa: Ana Zargin Gwamnoni 6 na da Laifi a Batun Sace Daliban Oyo a Najeriya
- Batun sace dalibai da malaman wata makarantar sakandire a jihar Oyo na ci gaba da jawo martani daga daidaikun mutane da kungiyoyi
- Kungiyar yarbawa ta AYDM ta zargi gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma da yi wa harkar tsaro rikon sakainar kashi a yankin
- AYDM ta yi ikirarin cewa gwamnonin suna da hannu da duk abubuwan da ke faruwa a yankin saboda gaza daukar matakan kariya tun farko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo, Nigeria - Ƙungiyar haɗin kan kabilar yarbawa ta AYDM ta zargi gwamnonin shiyyar Kudu maso Yamma da sakaci a harkar tsaro, wanda suka ce shi ya jawo sace dalibai a jihar Oyo.
Gwamnoni shida na Kudu maso Yamma dai sune Seyi Makinde (Oyo), Lucky Aiyedatiwa (Ondo), Biodun Oyebaniji (Ekiti), Dapo Abiodun (Ogun), Babajide Sanwo-Olu (Legas) da Ademola Adeleke (Osun).

Source: Facebook
An fara zargin gwamnoni 6 a Kudu
A rahoton da The Cable ta wallafa, AYDM ta ce gwamnonin shida sun gaza ɗaukar matakan kariya da suka dace da suka shafi tsaro a yankin, duk da alamun kwararar 'yan ta'adda da suka gani.
A wata sanarwa da sakataren ƙungiyar AYDM, Popoola Ajayi ya fitar, ƙungiyar ta ce gwamnonin ba su yi wani yunkuri ba tun 2010, duk da ayyukan ta'addancin da ke faruwa a jihohin da ke makwabtaka da su a Arewa ta Tsakiya.
Haka kuma, ƙungiyar ta koka da cewa hukumar tsaro ta Kudu maso Yamma, Amotekun, wadda aka kafa domin magance rashin tsaro a yankin, ba ta da isassun kayan aiki kuma ba za ta iya yaƙar ta'addanci yadda ya kamata ba.
Sakacin da aka yi a Kudu maso Yamma
Sanarwar ta ce:
"Sun ga duk alamomin abin da ke shirin faruwa, amma ba su yi komai ba. Zuwa yanzu an kashe manyan sarakunan Yarabawa guda huɗu sakamakon hare-haren 'yan ta'adda.
Kungiyar ta ba da misali da Oba Kehinde Falodun na Agamo da ke ƙaramar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo, wanda aka kashe a cikin fadarsa ranar 18 ga Fabrairu, 2026 bayan ya ƙi yarda yunƙurin garkuwa da shi.
"Irin wannan ƙaddara ita ma ta faɗa wa Oba Adegoke Adewusi, Olufon na Ifon wanda 'yan fashi da makami suka harbe shi har lahira a ranar 26 ga Nuwamba, 2020, a kan titin Ifon-Benin da ke yankin Elegbeka," in ji ta.

Source: Twitter
Kungiyar AYDM ta kuma yi ikirarin cewa babu ɗaya daga cikin gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma da ya ziyarci iyalai sarakunan gargajiyan domin yi mas jaje da ta'aziyya, in ji rahoton Vanguard.
Ƙungiyar ta ce sace ɗaliban makaranta da malamai daga ƙaramar hukumar Oriire a jihar Oyo ya tabbatar da "halin ko'in kula, sakaci da rashin nuna damuwa na shugabannina yankin."
Ana zargin Makinde kan sace daliban Oyo
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya yi zargin cewa Gwamna Seyi Makinde ne ya kitsa sace dalibai a Oyo dok bata sunan Shugaba Bola Tinubu.
Ya ce Makinde bai mayar da martani ko daukar matakin gaggawa ba bayan sace daliban, yana zargin cewa ya fi mayar da hankali kan harkokin siyasa fiye da magance matsalar.

Kara karanta wannan
Adelabu: Tsohon Ministan Tinubu ya tayar da kura kan zaben fitar da gwani na gwamna
Fayose ya ce ba a yin adalci wajen zargin shugaban kasa da matsalolin tsaro, alhali gwamnatocin jihohi ya kamata a rika jefa wa tambayoyi.
Asali: Legit.ng

