Abin Tausayi: Mutanen da Aka Sace Suna Ibada a Kwara Sun Mutu a Hannun 'Yan Bindiga
- Mutane biyar daga cikin masu ibada takwas da aka sace daga cocin ECWA da ke Omugo a jihar Kwara sun mutu a hannun 'yan bindiga
- Rahotanni sun nuna cewa matar Faston cocin, Misis Rachael Oluwaremilekun Omole, tana cikin wadanda suka rasa rayukansu
- Har yanzu mutum uku na ci gaba da zama a hannun masu garkuwa bayan sama da watanni biyu a tsare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kwara, Nigeria - An tabbatar da mutuwar mutane biyar daga cikin masu ibada takwas da aka sace a wani hari da aka kai cocin ECWA da ke Omugo, yankin Oro Ago, a karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara.
Faston cocin, Rabaran Timothy Omole, ne ya sanar da mabiyansa wannan mummunan labari ta wani sako da ya fitar, inda ya bayyana cewa lamarin ya girgiza shi matuka.

Source: Original
Matar Fasto ta mutu a daji
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa daya daga cikin wadanda suka rasu ita ce matar Faston, Misis Rachael Oluwaremilekun Omole.
Sauran wadanda aka tabbatar da mutuwarsu sun hada da Cif David Omopariola, Cif Joseph Ibitoye Afariogun, Misis Iyabo Aniyi da kuma Dattijo Joshua Akanbi Adeyemi.
Rabaran Omole ya bayyana cewa daga cikin mutane takwas da aka sace daga cocin a ranar 22 ga Maris, 2026, mutum uku ne kawai suka rage a hannun masu garkuwar.
Ya ce:
"Cikin bakin ciki nake sanar da ku cewa daga cikin mutane takwas da aka sace daga cocin ECWA Omugo, mutum uku ne kawai suka rage a hannun masu garkuwa. Sauran biyar sun koma ga Ubangiji."
Yadda aka samu labarin mutuwarsu
A cewar Faston, wani daga cikin wadanda aka sace mai suna Sunday Bakare ne ya kawo labarin bayan ya samu damar tserewa daga hannun masu garkuwar bayan ya shafe sama da wata guda a tsare.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Cutar kwalara ta kama mutane sama da 4,000 a Borno, an rasa rayuka
Bakare ya shaida wa cocin cewa mutane biyar daga cikin wadanda aka sace sun mutu, yayin da mutum uku ke ci gaba da zama a hannun masu garkuwar.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin wadanda aka sace na fama da matsalolin lafiya kuma suna shan magunguna kafin a yi garkuwa da su.

Source: Facebook
Sai dai an zargi masu garkuwar da hana su samun magungunan da suke bukata, lamarin da ake zargin ya taimaka wajen janyo mutuwar wasu daga cikinsu.
An kai harin ne a ranar 22 ga Maris, 2026, lokacin da wasu yan bindiga dauke da makamai suka kutsa cikin cocin yayin da ake gudanar da ibada.
Maharan sun rika harbe-harbe domin tarwatsa masu ibada kafin daga bisani su yi awon gaba da mutum takwas zuwa cikin daji, kamar yadda Punch. Ta kawo.
Yan bindiga sun kona fadar Sarki
A wani rahoto, kun ji cewa fargaba ta mamaye Yashikira bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari fadar sarki tare da sace matansa da wasu daga cikin ‘ya’yansa a Kwara.
Wani mazaunin yankin mai suna Nasiru ya ce maharan sun kutsa cikin fadar masarautar Yashikira inda suka banka wa wasu sassan fadar wuta.
Majiyoyi daga yankin sun ce 'yan ta'addar sun lalata ɗakuna da dama a cikin fadar tare da ƙona motoci a yayin wannan harin.
Asali: Legit.ng
