Lokuta 3 da Babachir Lawal Ya Canza Gidan Siyasa daga Mulkin Buhari zuwa Yau
FCT, Abuja - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya sake tsintar kansa a mazaunin da ya saba kasancewa, wato a tsakiyar rigimar siyasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Babachir Lawal ya sake daukar hankali bayan da ya yi murabus daga jam'iyyar ADC a ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2026.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta ce ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na jam'iyyar domin fifita tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
Babachir ya sha sauya gidan siyasa
Cikin shekaru da dama, Babachir Lawal ya gina suna a matsayin ɗan siyasar da ƙawance ba ya dorewa a tare da shi, ya saba sauyawa daga mai goyon baya zuwa mai suka cikin gaggawa da ban mamaki.
A duk tsawon siyasarsa, akwai wani tabbataccen tsari guda ɗaya dake bayyana. Babachir Lawal ya sha sauyawa daga aboki, ya rikida lokaci guda zuwa mai suka.
Lokutan da Babachir ya sauya gida a siyasa
Tsohon injiniyan ya kare Muhammadu Buhari kafin su sami saɓani da wasu jiga-jigai a cikin APC. Ya fito ya yaƙi Tinubu bayan da can baya ya taɓa goyon bayansa.
Ya rungumi Obi kafin daga baya ya bar shi. Ya shiga ƙungiyar haɗin gwiwa ta ADC kafin daga baya ya juya wa Atiku baya.
A yanzu haka, yana nesanta kansa da Atiku da Obi, inda yake jaddada cewa ba ya son ya kasance cikin kowane irin tsarin siyasa.
Ga jerin lokutan da Babachir David Lawal ya canza sheka.
1. Daga abokin Tinubu zuwa mai sukarsa
A can baya, Babachir Lawal ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da suka fi kowa zakin murya.
Ya yi aiki a matsayin SGF a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma an ɗauke shi a matsayin daya daga cikin manyan masu fada a ji daga na Arewa a cikin tsarin jam'iyyar APC.
Jaridar Vanguard ta ce tsohon SGF ɗin ya taɓa jinjina wa Tinubu da Bisi Akande, tsohon shugaban riƙon kwarya na jam'iyyar APC na kasa, a baya saboda tallafa wa zamansa a matsayin sakataren gwamnatin tarayya a ƙarƙashin Buhari.
Amma dangantakar ta lalace daga baya lokacin da Tinubu ya zaɓi Shettima a matsayin abokin takararsa na mataimakin shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2023.
Biyo bayan shawarar Tinubu na zaɓar Shettima, wanda suke da addini ɗaya na Musulunci, a matsayin abokin takararsa, tsohon SGF ɗin ya janye goyon bayansa, inda ya jaddada cewa yana adawa da tsarin takarar Musulmi da Musulmi na jam'iyyar APC.
Kodayake ya ci gaba da taka rawa a fagen siyasa, a hankali Babachir Lawal ya zama ɗaya daga cikin masu sukar Tinubu.
Gabannin zaɓubbukan 2023, ya yi adawa da burin takarar shugabancin ƙasa na Tinubu kuma ya fito fili ya marawa Peter Obi baya.
2. Ya goyi bayan Peter Obi kafin su rabu
Ƙawancen Babachir Lawal da Peter Obi ya nuna alamun samun nasara a farko, amma daga baya sun rabu.
Babachir ya sha yaba wa tsohon gwamnan na Anambra akai-akai kuma ya shiga cikin ƙoƙarin neman goyon bayan Arewa ga ɗan takarar na jam'iyyar LP a zaben 2023.
Yayin da aka fara samun sababbin dabarun sauya sheka na siyasa gabanin 2027, Babachir Lawal ya fice daga sansanin Obi kuma ya shiga cikin tafiyar haɗaka ta ADC, wadda daga ƙarshe ta samar da Atiku a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa.
Ba a dade ba aka fahimci har yanzu tsohon sakataren gwamnatin tarayyan bai huce daga caccakar Peter Obi, People Gazette ta rahoto shi yana cewa 'dan siyasar na neman takara a bagas.
3. Hadewa da Atiku kafin ya koma sukarsa
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Babachir Lawal duka 'yan jihar Adamawa ne.
A Adamawa, wasu masu ruwa da tsaki na ADC suna ɗaurawa Babachir laifin ficewar fitattun 'yan siyasa da dama, ciki har da Aishatu Binani da Ishaku Abbo, waɗanda suka bar jam'iyyar zuwa jam'iyyun LP da NDC.
Tsawon watanni, Babachir ya shiga cikin harkokin siyasa a cikin ADC kuma an ɗauke shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan da ke tallafa wa ƙoƙarin gina jam'iyyar domin ta zama ƙarƙashin tsarin hamayya mai ƙarfi.

Source: Twitter
Amma bayan da Atiku ya samu tikitin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC da ƙuri'u 1,846,370, inda ya doke Rotimi Amaechi da Mohammed Hayatu-Deen, farat ɗaya Babachir ya juya wa tafiyar baya.

Kara karanta wannan
Shugaban Obidients ya tabo batun 'rusa' masallacin Peter Obi lokacin da yake gwamna
Ya zargi mutanen Atiku da yin babakere a harkar zaben fitar da gwanin da kuma tafka magudi wanda hakan ya sanya ya samu nasara, tashar Channels tv ta kawo rahoton.
Babachir ya bayyana cewa Atiku zai zama shugaban kasa mara katabus wanda al'amura za su tabarbare a karkashinsa fiye da Shugaba Bola Tinubu.
Hakazalika, ya bayyana cewa zai yi aiki domin ganin Atiku bai zama shugaban kasa ba a zaben 2027. Sai dai a baya ya soki Tinubu da Obi, za a ga wanda zai marawa baya.
Babachir ya zargi Tinubu da iya murde zabe
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da gwanancewa wajen iya murde zabe.
Babachir Lawal ya bayyana cewa zai yi matuƙar wahala a kifar da APC a zaben shugaban kasa na 2027 idan har abin da ke tabbatar da nasara shi ne maguɗin zaɓe.
Tsohon SGF din ya yi zargin cewa shugaban ƙasar zai yi amfani da dabarun murɗe zaɓe wajen rinjayar sauran ’yan takara a babban takarar da za a yi a farkon badi.
Asali: Legit.ng


