Datti Baba Ahmed Ya Fadi Dalilin Aiki da Peter Obi a 2023, 'Yan Siyasa 3 Sun Guje Shi'
- Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya tuna baya kan takarar da ya yi tare da Peter Obi
- Yusuf Datti Baba-Ahmed ya bayyana cewa Peter Obi ya sha wuya wajen neman abokin takara domin har 'yan siyasa uku ne suka guje shi
- Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa tausayawa ce ta sanya ya yi aiki tare da tsohon gwamnan na jihar Anambra
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Yusuf Datti Baba-Ahmed, tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen shekarar 2023, ya yi magana kan takararsa tare da Peter Obi.
Yusuf Datti Baba-Ahmed ya bayyana cewa ya yi haɗin gwiwa ne tare da Peter Obi a zaben shekarar saboda tausayin da yake yi masa.

Source: Twitter
Yusuf Datti Baba-Ahmed ya yi wannan bayani ne a lokacin wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Symfoni, wadda @emmaikumeh ya sanya a shafinsa na X a ranar Laraba, 3 ga watan Yunin 2026.
Me Datti Baba-Ahmed ya ce kan Peter Obi?
Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasar ya ce Peter Obi ya tuntuɓi fitattun 'yan siyasa guda uku gabanin zaɓen 2023, amma babu ko guda ɗaya da ya amince ya yi takara tare da shi.
A cewarsa, shawararsa na zama abokin takarar Obi ta samo asali ne saboda tausayawa tsohon gwamnan na Anambra da kuma yanayin siyasar ƙasar a wancan lokacin.
“Mutane ba su gane cewa tsakanina da Obi, akwai babban mataki na tausayi ba. Ina tausaya masa. Kuma wannan tausayi shi ne jigon dangantakarmu."
“Lokacin da ya tuntuɓi wasu manyan 'yan siyasa guda uku a shekarar 2022, da na yi farin ciki da a ce ɗaya daga cikinsu ya yi takara tare da Peter Obi a 2022. Amma duka sun kauce masa. Na ji masa babu daɗi, kuma na ji ba daɗi ga Najeriya a matsayinta na ƙasa.”
- Yusuf Datti Baba-Ahmed
Baba Ahmed ya yi magana kan takara da Obi
Yusuf Datti Baba-Ahmed ya ce ya shiga cikin lamarin takarar ne da son ransa saboda ya yi amannar cewa yin hakan shi ne mafi alheri ga makomar ƙasar.
“Na ɗauki nauyin hakan a karan kaina domin a dabi'ance na kasance mai mika kaina a kowane lokaci. Saboda dacewar Najeriya, na miƙa wannan tausayi gare shi."
- Yusuf Datti Baba-Ahmed

Source: Twitter
Dukkanin 'yan siyasar biyu sun fice daga jam'iyyar LP wadda suka yi takara a karkashinta a zaben 2023, inda suka koma jam'iyyun PRP da NDC.
Batun Peter Obi ya rusa masallaci
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kungiyar Obidients Movement, Yunusa Tanko, ya yi magana kan zargin cewa Peter Obi ya rusa masallaci lokacin da yake Gwamnan Anambra.
Yunusa Tanko, ya yi watsi da zargin cewa ɗan takarar na kujerar shugaban ƙasa a jam'iyyar NDC, ya rushe masallaci a lokacin da yake gwamnan jihar Anambra.
Shugaban na kungiyar Obidients ya jaddada cewa iƙirarin ƙarya ne kuma babu wata shaidar da ake da ita da ke goyon bayan zancen.
Asali: Legit.ng

