Netanyahu Ya Yi Magana kan Takaddamarsa da Trump, Ya Fadi Halin da Alakarsu Ke Ciki
- Firaministan Israila, Benjamin Netanyahu, ya yi magana kan sabanin da suka samu da Shugaba Donald Trump na Amurka
- Benjamin Netanyahu ya rage kaifin takaddamar inda ya nuna cewa shi da Trump suna kan matsaya daya dangane da Hezbollah
- Firaministan na Israila ya nuna cewa dama ana samun sabani kan dabarun yaki, amma ana samun hanyar daidaita al'amura
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tel-Aviv, Israila - Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya rage muhimmancin takaddamar da ke tsakaninsa da Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump.
Netanyahu ya ce duka su biyun suna da ra'ayi ɗaya a kan manufar kwacewa dakarun Hezbollah makamai domin samun zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Lebanon.

Source: UGC
Netanyahu ya rage girman wannan takaddama a cikin wata hira da ya yi da tashar CNBC a ranar Laraba, 3 ga watan Yunin 2026.
Trump ya tabbatar da cewa sun yi cacar baki mai zafi da Netanyahu, inda aka ruwaito cewa ya daka masa tsawa tare da amfani da munanan kalaman zagi.
Me Netanyahu ya ce kan Trump?
Firaministan na Israila ya ce shi da Trump suna kan shafi ɗaya idan aka zo batun tunkarar ƙungiyar dakarun Hezbollah ta Lebanon.
"Hezbollah wata ƙungiya ce da Iran ke amfani da ita wadda ta sa daukacin mazauna Lebanon cikin hadari kuma take amfani da Lebanon a matsayin dandalin harba makamai masu linzami na ta'addanci zuwa biranenmu, da kuma harba jiragen yaƙi marasa matuƙi masu karkashe mutane a kan fararen hularmu."
“Saboda haka, idan muna son ceton Lebanon, idan muna son samun zaman lafiya tsakanin Lebanon da Isra'ila, kamar yaddda nake buƙata, dole ne mu kwace wa Hezbollah makamai kuma dole ne mu hana kasancewar dakarun soja a Lebanon."
"Kuma na san cewa wannan manufa ce da Shugaban Ƙasar da ni muke da ita baki ɗaya, kuma abin da ya kamata mu yi ke nan.”
- Benjamin Netanyahu
Netanyahu na fahimtar juna da Trump
Netanyahu ya bayyana cewa da shi da Trump a kowane lokaci suna samun fahimtar juna, inda ya ƙi yin ƙarin bayani daki-daki kan tattaunawar tasu.
“Muna da yarjejeniyoyi da dama, mun amince a kan manyan abubuwa. Ana samun waɗannan saɓani na dabarun aiki. A kowane lokaci muna samun hanyar daidaita su, kuma muna yin hakan a matsayin manyan abokai."
"Za mu iya saɓawa da safe, amma idan ya kai da yamma, sai mu samu fahimtar juna."
- Benjamin Netanyahu

Source: Getty Images
Ya dangantakarsu take?
Yayin da aka tambaye shi ko dangantakarsa da Trump ta sauya, Netanyahu ya ce:
“A'a annan ta kasance kyakkyawar dangantaka, domin ya kasance babban aboki mafi girma da Isra'ila ta taɓa samu a Fadar White House."
Netanyahu ya tattauna da Trump
A wani labarin kuma, kun ji cewa firaministan Israila, Benjamin Netanyahu, ya tattauna da Shugaba Donald Trump ta wayar tarho.
Benjamin Netanyahu ya ce shi da shugaban Amurka Donald Trump sun tattauna kan yaki da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.
Firaministan na Israila ya ce sun amince cewa duk wata yarjejeniya da Iran dole ta kawo karshen barazanar nukiliya gaba daya.
Asali: Legit.ng

