Abu Ya Girma: Hakeem Baba Ahmed Ya Bukaci Shugaba Tinubu Ya Yi Murabus
- Jam’iyyar PRP ta bukaci Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus daga mukaminsa saboda tabarbarewar tsaro a Najeriya
- Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Hakeem Baba-Ahmed ya zarge shi da gazawa wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya
- PRP ta ce matsalar tsaro ta kara ta’azzara a fadin kasar nan karkashin mulkinsa, tana mai kira ga yan Najeriya da su hada ka su kare kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawonBshekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jam’iyyar adawa ta PRP ta bukaci Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi murabus daga mukaminsa.
PRP ta ce ya kamata Shugaba Tinubu ya yi murabus ne saboda ya gazawa wajen sauke babban nauyin da kundin tsarin mulki ya dora masa na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Source: UGC
Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Hakeem Baba-Ahmed, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.
Ya ce kasar nan na fuskantar mummunar matsalar tsaro da ta sanya rayuwar al’umma cikin hadari.
PRP ta ce babu wanda ke cikin aminci
A cewar Baba-Ahmed, Najeriya na cikin wani mawuyacin hali, domin a halin yanzu babu wani dan kasa da zai iya cewa yana cikin cikakken tsaro.
Ya ce masu aikata laifuffuka sun kara karfi a sassa daban-daban na kasar nan, yayin da hare-hare, kashe-kashe da garkuwa da mutane ke ci gaba da karuwa.
"Babu shakka Shugaba Bola Tinubu ya gaza wajen sauke nauyin kare ‘yan Najeriya.
"A karkashin mulkinsa, tsofaffin matsalolin tsaro sun kara muni, yayin da ‘yan kasa ke fadawa hannun miyagu ba tare da la’akari da matsayi ko shekaru ba," in ji shi.
Hare-hare sun karu a makarantun Najeriya
Shugaban na PRP ya nuna damuwa kan yadda makarantu suka zama sababbin wuraren da masu garkuwa da mutane ke kai hare-hare.
Ya ce yanzu yara dalibai da malamai suna cikin wadanda ake kai wa hari, lamarin da ya nuna yadda matsalar tsaro ta bazu zuwa kusan ko'ina cikin kasar.
Daga Bama a jihar Borno zuwa Badagry a jihar Legas, Baba-Ahmed ya ce babu wani yanki da za a iya cewa ya tsira daga hare-haren masu aikata laifuka.
PRP ta nemi Tinubu ya yi murabus
Jam’iyyar PRP ta bukaci ‘yan Najeriya su hada kai domin neman kawo karshen abin da ta kira gazawa da halin ko-in-kula daga gwamnatin tarayya.

Source: Facebook
Baba-Ahmed ya ce a kasashen da dimokuradiyya ta kafu sosai, shugaban da ya gaza irin wannan ba zai ci gaba da zama kan mulki ba, kamar yadda Punch ta rahoto.
Ya kara da cewa:
"Shugaba Tinubu ya tattara dukkan karfin iko a hannunsa, amma ya kasa amfani da shi wajen kare rayukan ‘yan Najeriya. Saboda haka muna ganin lokaci ya yi da zai yi murabus yanzu."
Atiku ya soki Tinubu kan matsalar tsaro
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar , ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matsalar rashin tsaro.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya nuna cewa ana sanya 'yan Najeriya cikin zullumi da fargaba saboda rashin tsaro.
Atiku ya soki Tinubu ne yayin da ya mayar da martani game da labarin sace 'yar uwa da kuma tagwayen yayar tsohon Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu .
Asali: Legit.ng

