'Yan Bindiga Sun Sace Dalibai a Jihar Zamfara ana Jimamin Abin da Ya Faru a Oyo
- 'Yan bindiga sun yi aika-aika, ana zargin sun sace wasu dalibai a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
- Tsagerun 'yan bindigan sun sace daliban ne na makarantar kimiyya da fasaha ta tarayya da ke a karamar hukumar Kaura Namoda
- Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta bayyana cewan an turo jami'an tsaro domin su ceto daliban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Wasu da ake zargi 'yan bindiga ne sun sace ɗalibai bakwai na Makarantar kimiyya da fasaha ta tarayya (Federal Polytechnic), da ke Kaura Namoda a jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun sace daliban ne bayan sun afka wa rukunin gidajensu na wajen makaranta da ke gefen rukunin gidaje na Low-Cost a garin Kaura Namoda.

Source: Facebook
Shugaban karamar hukumar Kaura Namoda, Hon. Mannir Haidara Kaura, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust.
'Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai
Hon. Mannir Haidara Kaura ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun ƙaddamar da ayyukan ceto domin tabbatar da dawo da ɗaliban da aka sace cikin koshin lafiya.
“Lamarin ya faru, kuma a halin yanzu jami'an tsaro suna gudanar da ayyukan ceto domin tabbatar da dawo da ɗaliban da aka sace cikin koshin lafiya."
- Mannir Haidara Kaura
Ɗaya daga cikin ɗaliban makarantar, Ibrahim Ahmad, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin ɗaliban da aka sacen ya yi nasarar guduwa, inda aka bar ɗalibai maza uku da mata uku har yanzu a hannun 'yan bindigan.
'Yan sandan Zamfara sun yi bayani
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da sace ɗaliban, inda bayyana cewa jami'an tsaro sun tsananta ƙoƙari domin ceto waɗanda abin ya shafa.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce lamarin ya faru ne a gidan ɗaliban da ke gefen rukunin gidaje na Low-Cost a Kaura Namoda.

Kara karanta wannan
Dattawan Kwara sun yi barazana da 2027 bayan kashe masu mutum 1200 a mulkin Tinubu
Ya tabbatar da cewa ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa ya gudu, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran ɗalibai shida da suka rage, Daily Post ta kawo labarin.
Yadda aka sace dalibai a Zamfara
Yayin da yake bayanin yadda lamarin ya faru, Yazid Abubakar ya ce an bayyana cewa ɗaya daga cikin ɗaliban ya fita waje da daddare domin ya yi fitsari, kuma cikin rashin sani ya bar ƙofa a buɗe.
“Ɗaya daga cikin ɗaliban ya fita waje a cikin dare, yana cewa yana son yin fitsari. A cikin yin hakan, ya bar ƙofa a buɗe. Cikin tsautsayi, sai 'yan bindiga da ke wucewa ta yankin suka shiga gidan kuma suka sace ɗaliban."
- DSP Yazid Abubakar

Source: Original
'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun sake kai hari a wani kauyen da ke jihar Sokoto.
Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan, waɗanda suka zo da yawa a kan babura, sun farmaki kauyen ne da misalin ƙarfe 8:00 na safe.
Aƙalla mutane 20 ne aka kashe a lokacin sabon harin, yayin da aka ƙona gidaje da dama sannan wasu mutane da dama ba a gansu ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
