2027: NDC Ta Jawo Tsohon Shugaban Matasan APC, Ta Tsaida Shi Takarar Gwamna a Gombe

2027: NDC Ta Jawo Tsohon Shugaban Matasan APC, Ta Tsaida Shi Takarar Gwamna a Gombe

  • Tsohon shugaban matasan APC na ƙasa, Sadiq Abubakar, ya lashe tikitin takarar gwamna na jam'iyyar NDC a jihar Gombe
  • Sadiq Abubakar ya ce ya bar APC ne saboda matsin tattalin arziki da rashin gamsuwa da manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Matashin 'dan siyasar ya kuma yabawa jam'iyyar NDC bisa yadda ta yi kokarin tabbatar da adalci da dimokuraɗiyya a zaɓen fitar da gwani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe, Nigeria. - Tsohon shugaban matasan jam'iyyar APC na ƙasa, Sadiq Abubakar, ya zama ɗan takarar gwamna na jam'iyyar NDC a jihar Gombe gabanin zaɓen 2027.

Sadiq Abubakar ya sanar da nasararsa ne yayin da yake zantawa da manema labarai a jihar Bauchi ranar Laraba bayan kammala zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar.

NDC .
Tutar jam'iyyar adawa a Najeriya watau NDC Hoto: NDC Party
Source: Facebook

Dalilin ficewar Sadiq Abubakar daga APC

Kara karanta wannan

Bayan ficewar Babachir, sabuwar rigima ta bullo a ADC a jihar Adamawa

Fitowarsa a matsayin ɗan takarar gwamna ta zo ne makonni kaɗan bayan ya yi murabus daga APC, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

A lokacin da ya fice daga jam'iyya mai mulki, Sadiq Abubakar ya bayyana cewa matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake fama da su a ƙasar nan sun taka rawa wajen yanke shawarar barin APC.

Ya kuma nuna rashin gamsuwa da wasu manufofi da shirye-shiryen gwamnatin APC, yana mai cewa akwai buƙatar sabon salo na siyasa da zai ba jama'a damar samun wakilci na gari.

Abubakar ya gode wa magoya baya

Da yake tsokaci kan nasarar da ya samu, Sadiq ya miƙa godiyarsa ga shugabannin NDC, wakilai da magoya bayan jam'iyyar bisa amincewar da suka nuna masa.

"Wannan karramawa ba tawa kaɗai ba ce, ta shafi matasa masu neman dama, manoma masu fafutukar samun ingantacciyar rayuwa, iyaye mata masu fatan ganin makoma mai kyau ga 'ya'yansu da kuma al'ummomin da ke neman ci gaba," in ji shi.

Sadiq Abubakar ya kuma yaba wa jam'iyyar NDC bisa abin da ya kira tsayawa kan gaskiya da dimokuraɗiyya a yayin gudanar da zaɓen tsaida gwani, cewar rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Bayan sukar APC, ADC da NDC, Babachir ya fadi wanda zai zaba a 2027

Sadiq.
Tsohon shugaban matasan APC, Sadiq Abubakar tare da jagoran NDC na kasa, Sanata Serieke Dickson Hoto: NDC Party
Source: Facebook

Alkawarin haɗa kan jama'a

Abubakar ya yi alƙawarin yin aiki tare da shugabanni, magoya baya da sauran masu ruwa da tsaki a faɗin jihar Gombe domin gina ginshikin da zai kawo ci gaba da kyakkyawan shugabanci.

Ya ce burinsa shi ne samar da gwamnati mai gaskiya, wacce za ta mayar da hankali kan walwalar jama'a, bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi ga matasa da kuma inganta rayuwar al'ummar jihar Gombe.

NDC ta tsaida dan takara a Zamfara

A baya, kun ji cewa jam'iyyar NDC ta ayyana Sanata Kabiru Marafa a matsayin dan takarar gwamnan jihar Zamfara a babban zaben 2027.

Sanata Marafa ya samu tikitin jam’iyyar ne ta hanyar maslaha bayan kasancewarsa shi kaɗai ya nemi takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar NDC.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan ayyana shi a matsayin ɗan takarar gwamna, Sanata Kabiru Marafa ya gode wa shugabanni da ‘ya’yan jam’iyyar bisa amincewa da suka nuna masa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262