Babbar Magana: Yadda Aka Yi Yunkurin Tayar da Bam a Gidan Gwamnatin Ondo
- Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya tuno yadda wasu matasa suka yi yunkurin tayar da bam a gidan gwamnatin jihar a baya
- Lucky Aiyedatiwa ya bayyana cewa jami'an tsaro sun yi kokari sosai bayan sun samu bayanan sirri kan shirin na matasan
- Gwamnan ya nuna cewa ana gudanar da ayyuka da dama domin ganin cewa an magance matsalar rashin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya bayyana yadda jami'an tsaro suka dakatar da wani shirin tayar da bam a gidan gwamnatin jihar.
Gwamna Aiyedatiwa ya ce ana zargin wasu matasa ne suka yi yunkurin tayar da bam a gidan gwamnatin jihar Ondo.

Source: Twitter
Aiyedatiwa ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a shirin 'Politics Today' na tashar Channels TV a ranar Alhamis, 4 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan
Da gaske 'yan bindiga sun sako dalibai da malamai da suka sace a Oyo? Bayanai sun fito
An dakile yunkurin tayar da bam a Ondo
Gwamnan ya bayyana dakile yunkurin tayar da bam din a matsayin ɗaya daga cikin nasarorin tsaro da dama da aka samu a jihar a cikin watannin baya-bayan nan.
A cewar Aiyedatiwa, rahotannin sirri da aka samu kimanin watanni uku zuwa huɗu da suka gabata, sun ankarar da hukumomin tsaro game da wasu ayyuka da suka shafi wasu matasa waɗanda ake zargi suna tsara wani hari a gidan gwamnati.
Ya ce da farko waɗanda ake zargin sun sauka ne a wani masauki kafin daga baya su koma wani gida na haya, inda ake zargin sun ci gaba da shirye-shiryen gudanar da aikin da suka tsara.
Yadda aka hana dasa bam a gidan gwamnati
Sakamakon aiki da bayanan sirrin da aka samu, jami'an tsaro, ciki har da jami'an 'yan sanda da na rundunar Amotekun, sun kai samame wurin kuma suka kama waɗanda ake zargin.
A lokacin gudanar da aikin, an samu kayayyaki da na'urori da ake amannar suna da alaƙa da shirin tayar da bam ɗin.

Kara karanta wannan
An fara jita jitar cewa Sheikh Abdulmudallib ya samu tikitin takarar gwamna a 2027
“Bayan samun rahotannin sirri, 'yan sanda da Amotekun sun motsa, suka kai samame wurin, suka kama waɗanda ake zargin, kuma har yanzu suna tsare."
- Gwamna Lucky Aiyedatiwa
Gwamna Aiyedatiwa ya ce ana kokari kan tsaro
Aiyedatiwa ya nuna cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin tantance makasudin shirin yunkurin tayar da bam din.
Ya ƙara da cewa lamarin yana nuna ƙalubalen tsaro da ke fuskantar jihar da kuma muhimmancin gudanar da ayyukan daukar mataki ta hanyar tattara bayanan sirri.

Source: Original
Gwamna ya ce nasarar gudanar da aikin tana nuna cewa nasarorin tsaro da dama galibi ba a lura da su saboda ana hana aukuwar hare-hare kafin su faru.
“Ana gudanar da ayyuka da dama. Tsaro wani nauyi ne guda ɗaya da shugabanni ke ɗauka wanda ba kowa ne ke iya ganinsa ba. Sai kawai idan an samu kuskure ko sakaci za a dinga gani kamar gwamnati ba ta yin abin da ya dace. Muna yin abubuwa da dama."
- Gwamna Lucky Aiyedatiwa
'Yan bindiga sun sace dalibai
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Ana zargin gwamnoni 6 na da laifi a batun sace daliban Oyo a Najeriya
'Yan bindigan sun sace ɗalibai bakwai na makarantar kimiyya da fasaha ta tarayya (Federal Polytechnic), da ke Kaura Namoda a jihar Zamfara.
Tsagerun 'yan bindigan sun sace daliban ne bayan sun afka wa rukunin gidajensu na wajen makaranta da ke gefen rukunin gidaje na Low-Cost a garin Kaura Namoda.
Asali: Legit.ng