Manyan Labarai A Yau
Jagoran 'yan bindigan da suka yi garkuwa da tsohon janar a jihar Katsina ya tuntubi iyalansa. Ya bayyana cewa yana so gwamnati ta cika masa wasu bukatu.
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya dauki matakin ladabtarwa kan wasu daga cikin hadimansa. An bayyana cewa an dakatar da hadiman ne sai baba ta gani.
Jam'iyyar APC mai mulki ta sanar da dakatar da dan majalisar wakilai na mazabar Auyo/Hadejia/Kafin Hausa, Hon. Usman Ibrahim kan wasu zarge-zarge.
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta sanar da daukar matakin hade wasu ma'aikatu wuri guda karkashin jagorancin kwamishina.
'Yan bindiga sun kai harin ta'addanci wanda ya yi sanadiyyar hallaka mutane da dama a jihar Sokoto. 'Yan bindigan kashe mutane ciki har da masu yawon Sallah.
Shugaban kungiyar Obidients Movement, Yunusa Tanko, ya yi martani kan batun cewa Peter Obi, ya rusa masallaci lokacin da yake kan kujerar gwamnan Anambra.
Daya daga cikin wadanda suka fafata a zaben fitar da gwani na takarar shugaban kasa a ADC, Mohammed Hayatu-Deen, ya ce ba zai je kotu ba kan zaben.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2027, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan jita-jitar cewa zai jagoranci zanga-zanga kan rashin tsaro.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya yi ikirarin cewa an tafka magudi a zabukan fitar da gwanin ADC da aka yi, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari