Magana Ta Fito: Dalilin da Ya Sa Donald Trump Ya Zazzagi Benjamin Netanyahu
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa ya kalamai masu kaushi kan Benjamin Netanyahu
- Mai girma Donald Trump ya tabbatar da cewa ya bayyana cewa ya yi kalaman kan Netanyahu saboda yakin da yake yi a kasar Lebanon
- Sai dai, duk da hakan, Shugaba Trump na kasar Amurka ya bayyana cewa yana da kyakkayawar alaka da Firaministan na Israila har yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya tabbatar da cewa an yi cacar baki mai zafi tsakaninsa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
An dai ruwaito cewa ya daka wa na-kusa da shi kuma abokin tafiyarsa tsawa tare da amfani da munanan kalaman zagi.

Source: Getty Images
A cikin wata hira da aka wallafa ranar Laraba, 3 ga watan Yunin 2026 a tashar New York Post, an tambayi Trump game da tattaunawar da suka yi da Netanyahu ta wayar tarho a ranar Litinin.
An tambayi Trump kan zagin Netanyahu
Wanda suke tattauna wa da Trump yayin hiran ya yi masa tambayar cewa:
“Ka ce, ‘Shin ka haukace ne? Me ka ke yi da gangan? Na taimake ka ka kauce wa shiga gidan yari.’ Shin wannan gaskiya ne? Shin ka yi magana da shi da waɗannan kalaman?”
Trump ya ba da amsa da cewa:
“Na yi. Na ɗan damu ƙwarai da gaske game da gaba da faɗan da yake yi akai-akai da kasar Lebanon. Na ce, ‘Bibi, dole ne mu dakatar da wannan."
Trump ya ci gaba da cewa yana da “kyakkyawar dangantaka sosai” da Netanyahu.
“Mun yi aiki mai kyau tare… Ina son Bibi sosai.”
- Donald Trump
Trump ya kausasa harshe kan Netanyahu
Shugaba Trump ya dankaro waɗannan munanan kalaman zagi ne saboda barazanar da Isra'ila ke yi na jefa bama-bamai a babban birnin Lebanon, wato Beirut.
Trump ya ji tsoron cewa hakan zai kawo cikas ga tattaunawar da ake yi da birnin Tehran na kawo ƙarshen yaƙi a Gabas ta Tsakiya.
Ofishin Netanyahu ya ƙi yin kowane irin sharhi game da tabbatar da waɗannan kalamai da Trump ya yi.

Source: Facebook
Ita kuwa Iran ta bayyana cewa ba za ta amince da kowace irin yarjejeniya da Amurka ba domin kawo ƙarshen yaƙin da Trump da Netanyahu suka ƙaddamar a ƙarshen watan Fabrairu, sai dai idan yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar ta haɗa da Ƙasar Lebanon.
Isra'ila dai ta mamaye Kudancin Lebanon a watan Maris 2026 domin neman dakarun Hezbollah masu ƙawance da Iran waɗanda suke kai hare-hare kan iyaka domin nuna goyon baya ga Tehran.
Trump ya hana Netanyahu kai hari
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya yi magana da Benjamin Netanyahu domin ka da ya kai hari a Lebanon.
Trump ya ce ya yi magana da kungiyar Hezbollah ta Lebanon kuma ya samu alkawarin cewa ba za ta kai hari kan Isra’ila ba.
Shugaban na Amurka ya kuma ce ba za a tura sojoji zuwa Beirut ba, yayin da duk sojojin da suke kan hanyarsu tuni aka mayar da su baya.
Asali: Legit.ng

