Abin Ya Yi Muni: Sojan Najeriya da Matasan NYSC 4 Sun Bakunci Lahira a Hanyar Adamawa

Abin Ya Yi Muni: Sojan Najeriya da Matasan NYSC 4 Sun Bakunci Lahira a Hanyar Adamawa

  • Akalla mutum shida sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da sojoji da 'yan bautar kasa a jihar Adamawa
  • Rahotanni sun nuna cewa mutanen da suka mutu a hatsarin sun hada da 'yan bautar kasa (NYSC) hudu da wani sojan Najeriya
  • Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta ce ana gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin da bayanan wadanda lamarin ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Adamawa, Nigeria - Akalla mutum shida ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da motar sojoji da kuma motar haya kirar Hummer a kan hanyar Girei zuwa Song da ke jihar Adamawa.

Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya faru ne da misalin karfe 1:50 na rana a ranar Laraba, lamarin da ya haddasa gobara mai karfi da ta kona motar haya tare da kashe dukkan fasinjojin da ke cikinta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace tsohon shugaban APC, sun masa bidiyo yana neman agaji

Adamawa.
Taswirar jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Matasa 'yan NYSC 4 sun mutu a hadari

Daily Trust ta rahoto cewa shaidun gani da ido sun bayyana cewa motar sojojin tana kan hanyarta daga Gombi zuwa Yola, yayin da motar Hummer ke dauke da fasinjoji biyar daga Yola zuwa Mubi lokacin da hadarin ya auku.

Bayan karon da motocin biyu suka yi, motar Hummer ta kife sannan nan take ta kama da wuta.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Ngurore, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce:

"Abin takaici, dukkan fasinjoji biyar da ke cikin motar Hummer sun kone kurmus bayan motar ta kama da wuta sakamakon hadarin."

A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa hudu daga cikin wadanda suka mutu mambobin hukumar yi wa kasa hidima ta NYSC ne da aka tura aiki a jihar Adamawa.

Sunayen wasu daga cikin mamatan

Ngurore ya bayyana sunayen biyu daga cikin mamatan da suka hada da Suleiman Juliet da Usman Shuaibu, wadanda dukkansu 'yan asalin jihar Kaduna ne.

Kara karanta wannan

An samu hirar Trump da jami'ansa da ke nuna fargabar yaki da Iran

Ya ce ana ci gaba da kokarin gano sauran wadanda suka mutu tare da tuntubar iyalansu, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Jami'in 'yan sandan ya kara da cewa wani soja da ke cikin motar rundunar soji shi ma ya mutu a hadarin.

Yan sanda.
Dakarun 'yan sandan Najeriya a kan titi suna gudanar da ayyukansu na tsaro Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan sanda sun fara bincike

Ya bayyana cewa jami'an tsaro tare da masu aikin ceto sun garzaya wurin da lamarin ya faru domin kai dauki kuma tuni aka kai gawarwakin wadanda suka mutu zuwa asibiti a Yola.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce ana gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin tare da tabbatar da cikakkun bayanai kan dukkan wadanda abin ya shafa.

Mutane 16 sun mutu a hatsari a Kogi

A wani labarin, kun ji cewa akalla mutane 16 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Kogi.

Hatsarin ya afku ne lokacin da wata motar bas nau'in Toyota Hiace,nwadda ke tafiya daga Jos na jihar Filato zuwa Legas, ta sauka daga kan titi yayin da take tunkarar wata gada.

Hukumar FRSC ta bayyana cewa gajiya da kuma gudu fiye da ƙa'ida ne suka yi sanadin wannan mummunan hatsari da ya salwantar da rayuka

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262