Amurka Ta Tabbatar da Kulla Hadin Gwiwa, Za Ta Kara Kawo Hare Hare cikin Najeriya
- Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce kasarsa na ci gaba da hadin gwiwa da Najeriya wajen yaki da ta'addanci
- Rubio ya bayyana cewa hadin gwiwar ya haifar da kashe Abu-Bilal Al-Minuki, mataimakin shugaban kungiyar ISIS ta duniya
- Amurka ta ce tana damuwa da hare-haren da ake kai wa Kiristoci a Najeriya, wanda hakan ya sa ta fara kokarin kai dauki kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United states - Amurka ta tabbatar da cewa tana gudanar da aikin hadin gwiwa da Najeriya domin tabbatar da tsaro da kawar da ayyukan ta'addanci a kasar.
Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ne ya bayyana hakan, inda ya ce kasarsa na ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumomin tsaron Najeriya.

Source: Getty Images
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Rubio ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin zaman sauraron kasafin kudin ma'aikatar harkokin wajen Amurka na shekarar 2027.
Ministan ya yi bayanin kasafin kudin ma'aikatarsa ne a gaban kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar wakilan kasar da ke Washington DC.
Amurka ta yi hadin gwiwa da Najeriya
A yayin jawabinsa, Rubio ya ce akwai damuwa sosai kan matsalar tashin hankali da hare-haren da ake kai wa Kiristoci a Najeriya.
Sai dai ya ce Amurka na ci gaba da aiki kafada da kafada da jami'an tsaron Najeriya domin dakile ayyukan kungiyoyin ta'addanci.
Ya ce:
"A yanzu muna gudanar da hadin gwiwa sosai da gwamnatin Najeriya da hukumomin tsaronta wajen yaki da ta'addanci.
"Makonni kadan da suka gabata mun gudanar da wani farmaki tare, wanda ya yi sanadin kashe mutum na biyu mafi girma a kungiyar ISIS ta duniya da ke aiki daga cikin Najeriya, kuma wannan hadin gwiwa na ci gaba."
Yadda aka kashe Abu-Bilal Al-Minuki
A ranar 15 ga Mayu ne aka kashe Abu-Bilal Al-Minuki, wanda ake dauka a matsayin mataimakin shugaban kungiyar ISIS, a wani samamen hadin gwiwar Amurka da Najeriya suka kai maboyarsa da ke yankin Tafkin Chadi.
Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya taba bayyana Al-Minuki a matsayin daya daga cikin manyan shugabannin ta'addanci da ake zargi da jagorantar hare-haren da suka yi sanadin mutuwar Kiristoci da dama a Najeriya.
Shi ma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da mutuwar Al-Minuki, inda ya ce an kashe wasu manyan kwamandojin kungiyar tare da shi a yayin farmakin.

Source: Twitter
Marco Rubio ya tabbatar wa Majalisar dokokin Amurka cewa wannan aikin hadin gwiwa zai ci gaba tsakanin kasar da Najeriya domin kare rayukan kiristoci, kamar yadda tashar AIT ta rahoto.
Majalisar Amurka ta taka wa Trump birki
A wani labarin, an ji cewa majalisar wakilan Amurka ta kada kuri’ar umurtar shugaban kasa Donald Trump da ya janye sojojin kasar daga yaƙin da ake yi da Iran.
Wannan na ɗaya daga cikin ƙudurori biyu da ‘yan Democrat suka gabatar waɗanda Fadar White House ta yi adawa da su amma sukaNsamu karbuwa a majalisa.
Ƙudurin ya umurci Trump da ya janye sojojin Amurka daga duk wata arangama da Iran, sai dai idan majalisar dokoki ta ayyana yaƙi ko ta ba da izinin amfani da ƙarfin soja.
Asali: Legit.ng

