Da Gaske 'Yan Bindiga Sun Sako Dalibai da Malaman da Suka Sace a Oyo? Bayanai Sun Fito
- Gwamnatin jihar Oyo ta ce bidiyon da ke yawo na cewa an sako dalibai da malamai da aka sace a Oriire karya ne
- Kwamishinan yada labarai na jihar Oyo, Dotun Oyelade, ya ce har yanzu ana kokarin ceto wadanda aka sace
- Gwamnati ta bukaci jama'a su rika tantance sahihancin labarai kafin yada su, yana ami cewa babu dalibin da aka sako zuwa yanzu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo, Nigeria - Gwamnatin jihar Oyo ta musanta wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ke ikirarin cewa dalibai, yara makaranta da malamai da aka yi garkuwa da su daga makaranta a karamar hukumar Oriire sun samu 'yanci.
A cikin wata sanarwa, Kwamishinan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama'a na jihar, Prince Dotun Oyelade, ya bayyana cewa rahoton ba gaskiya ba ne.

Source: Facebook
A rahoton da Tribune Nigeria ta wallafa, kwamishinan ya ce bidiyon na dauke da bayanan da za su iya jefa jama'a cikin rudani tare da kara tada hankalin iyalan wadanda abin ya shafa.
Yan bindiga sun sako daliban Oyo?
Oyelade ya jaddada cewa sabanin abin da ake yadawa a shafukan sada zumunta, har yanzu wadanda aka yi garkuwa da su ba su dawo gida ba.
Ya ce gwamnatin jihar Oyo na ci gaba da gudanar da wasu tsare-tsaren sirri da hadin gwiwa da hukumomin tsaro domin tabbatar da an kubutar da su cikin koshin lafiya.
A cewarsa:
"Bidiyon da ke yawo cewa an sako wadanda aka sace a Oriire ba gaskiya ba ne. Gwamnatin Oyo na ci gaba da aiwatar da wasu matakai cikin sirri, kuma muna da kwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba za su haifar da sakamakon da ake fata."
An gargadi masu amfani da soshiyal midiya

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Mutanen da aka sace suna ibada a Kwara sun mutu a hannun 'yan bindiga
Kwamishinan ya bukaci jama'a, musamman masu amfani da kafafen sada zumunta, da su guji yada bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.
Ya ce yada jita-jita na iya kara tsananta damuwa da firgici a tsakanin al'umma tare da jefa iyalan wadanda aka sace cikin karin bakin ciki da tashin hankali, innji rahoton Punch.
Oyelade ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar Oyo ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an kubutar da daliban, yara makaranta da malamai da aka yi garkuwa da su.

Source: Original
Wane mataki gwamnati ta dauka?
Ya ce gwamnatin na aiki tare da jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin daukar dukkan matakan da suka dace wajen dawo da su gida cikin aminci.
Gwamnatin jihar ta roki jama'a da su kwantar da hankalinsu tare da dogaro da bayanan da suka fito daga hukumomin gwamnati game da cigaban da ake samu a wannan batu.
AYDM ta dora laifi kan gwamnoni 6
A baya, kun ji cewa kungiyar haɗin kan kabilar yarbawa ta AYDM ta zargi gwamnonin shiyyar Kudu maso Yamma da sakaci a harkar tsaro.
AYDM ta yi ikirarin cewa sakacin gwamnonin ne ya jawo yan ta'adda suka shiga yankin, har suka iya scae dalibai a wata makaranta a jihar Oyo.
AYDM ta ce gwamnonin shida sun gaza ɗaukar matakan kariya da suka dace da suka shafi tsaro a yankin, duk da alamun kwararar 'yan ta'adda da suka gani.
Asali: Legit.ng

