Manyan Labarai A Yau
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a jihar Sokoto. Hare-haren na 'yan bindiga sun jawo an kashe mutane da dama tare da raba su da muhallansu.
An samu barkewar wani rikicin manoma da makiyaya a jihar Bauchi. Mummunan rikicin ya jawo asarar rayukan mutane bakwai tare da kon gidaje masu tarin yawa.
Jam'iyyar APC mai mulki ta yi magana kan wani jerin sunaye da ke ikirarin cewa na 'yan takararta ne na kujerun sanatoxi a zaben 2027. Ta ce a yi watsi da shi.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya sanar da rage farashin takin zamani ga manoma. Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta biyan rabin kudin buhu ga manoma.
Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasara kan 'yan ta'adda a yankin Gabas ta Tsakiya. Sojojin sun ceto mutanen da aka sace.
Jam'iyyar PDP ta gamu da koma baya a majalisar wakilan Najeriya. Wasu 'yan majalisa guda hudu daga jihar Bauchi sun sanar da ficewarsu daga PDP zuwa jam'iyyar APM.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi kalamai masu kaushi kan majalisa bayan da ta umurci ya janye sojojin Amurka a yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika sunan Dr. Zainab Marwa ga majalisar dattawa domin tantancewa ta mamba a majalisar gudanarwa ta hukumar NDDC.
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan karuwar matsalar rashin tsaro. Atiku ya ce gwamnati ta kasa koyon darasi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari