Shugaba Tinubu Ya Yi Sabon Nadi a Gwamnatinsa, Ya Mika Sunan ga Majalisa

Shugaba Tinubu Ya Yi Sabon Nadi a Gwamnatinsa, Ya Mika Sunan ga Majalisa

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zabi Dr. Zainab Marwa domin zama mamba a majalisar gudanarwa ta hukumar kula da ci gaban yankin Niger Delta (NDDC)
  • Mai girma Bola Tinubu ya mika sunan ga majalisar dattawa domin tantancewa tare da amincewa da Dr. Zainab Marwa a sabon mukamin da yake son ta rike
  • Nadin na ta na zuwa ne domin ta cike gurbin tsohon mamban da ke rike da mukamin, wanda ya yi murabus domin neman takarar gwamnan jihar Adamawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi nadi a majalisar gudanarwa ta hukumar kula da ci gaban yankin Niger Delta (NDDC).

Shugaba Tinubu ya miƙa sunan Dr. Zainab Marwa ga Majalisar dattawa domin tabbatar da ita a matsayin mamba a majalisar gudanarwa ta NDDC, mai wakiltar shiyyar Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Hakeem Baba Ahmed ya bukaci Shugaba Tinubu ya yi murabus

Shugaba Tinubu ya yi nadi a hukumar NDDC
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa hakan na kunshe ne a cikin wata wasiƙa da shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta a ranar Alhamis, 4 ga watan Yunin 2026.

Akpabio ya karanta wasikar Tinubu

A cikin wasikar da Sanata Akpabio ya karanta a zauren majalisar, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa wannan naɗi ya biyo bayan tanadin da ke cikin dokar kafa hukumar NDDC, rahoton jaridar TheCable ya nuna hakan.

Naɗin an yi shi ne da nufin cike gurbin da aka samu sakamakon murabus ɗin tsohon mamban hukumar da ya gabata, Hon. Abdulrazak Namdas.

Hon. Abdulrazak Namdas ya sauka daga muƙaminsa a ranar 30 ga Maris, 2026, domin maida hankali kan burinsa na tsayawa takarar gwamna a jihar Adamawa.

Shugaba Tinubu ya nuna kyakkyawan zato cewa Majalisar Dattawa za ta duba tare da tabbatar da naɗin Dr. Zainab Marwa cikin gaggawa, domin ba hukumar damar ci gaba da gudanar da ayyukanta ba tare da tangarda ba na kawo ci gaba a yankin.

Kara karanta wannan

Akpabio: majalisar dattawa za ta ceto sanatocin APC da aka kwarfe

Tinubu na son a tabbatar da Dr. Zainab Marwa

Wani bangare na wasikar na cewa:

“Ana bukatar Majalisar Dattawa da ta lura cewa naɗin Dr Zainab Marwa an yi shi ne domin cike gurbin da ya samu sakamakon murabus din Namdas Abdulrazak, daga shiyyar Arewa maso Gabas, wanda ya yi murabus a ranar 30 ga watan Maris, 2026 domin tsayawa takarar gwamnan jihar Adamawa."
“A kan wannan gaba, ina da kyakkyawan zaton cewa Majalisar Dattawa za ta duba tare da tabbatar da naɗin Dr Zainab Marwa a matsayin mamba a majalisar gudanarwa ta hukumar kula da yankin Niger Delta (NDDC) domin wakiltar shiyyar Arewa maso Gabas.”

An miƙa sunan Zainab Marwa ga kwamitin Majalisar Dattawa kan Hukumar NDDC domin tantancewa da daukar sauran matakai na majalisa.

Shugaba Tinubu ya yi nadi a hukumar NDDC
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na jawabi a wajen taro Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

An bukaci Tinubu ya yi murabus

​A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar PRP mai adawa a Najeriya ta bukaci Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi murabus daga kan mukaminsa.

Kara karanta wannan

Babban Sarki a Zamfara da Matawalle sun yi addu'o'i ga Tinubu domin samun nasara

Jam'iyyar PRP ta ce ya kamata Shugaba Tinubu ya yi murabus ne saboda gazawar da ya yi wajen sauke babban nauyin da kundin tsarin mulki ya dora masa na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Shugaban jam'iyyar PRP na kasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce kasar nan na fuskantar mummunar matsalar tsaro da ta sanya rayuwar al’umma cikin hadari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng