Gwamna Alia Ya Saukakawa Manoma, Za Su Samu Taki a Farashi mai Rahusa
- Manoma za su samu taki a farashi mai rahusa bayan tallafin da gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, domin gudanar da noma
- Gwanna Hyacinth Alia ya rage farashin takin zamani ga manoma inda a yanzu za su biya N28,000 kan kowane buhu
- Ya bukaci mutanen da za su jagoranci aikin da su gudanar da shi cikin gaskiya da rikon amana ba tare da karkatar da shi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya sanar da cewa manoma a jihar za su sayi takin zamani a kan farashin tallafi na N28,000 a kowane buhu.
Gwamna Alia ya bayyana cewa za a sayi takin ne kan farashi mai rahusa a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin haɓaka ayyukan noma.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce Gwamna Alia ya yi wannan sanarwa ne ranar Alhamis, 4 ga watan Yunin 2026, yayin ƙaddamar da aikin sayarwa da rarraba takin zamani da kayan noma na shekarar 2026 a jihar.
Gwamna Alia ya rage farashin taki
Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta biya ragowar kuɗi N28,000 a kan kowane buhun takin zamani domin saukakawa manoma gabanin lokacin noma.
“Ina umartarku da ku gudanar da ayyukanku cikin gaskiya, kwarewa, da adalci. Kada a ba da damar karkatar da kaya, son zuciya, ko zalunci.”
“Kowane kayan noma da aka samo a ƙarkashin wannan shiri dole ne ya isa ga waɗanda aka yi dominsu. Tabbatar da gaskiya da riƙon amana za su kasance jagora a cikin wannan aiki.”
“Za a sayar da takin zamani a kan farashin tallafi na N28,000 a kowane buhu ga manoma, yayin da gwamnati za ta biya daidai ragowar kuɗi na N28,000 domin cika kuɗin buhun.”
- Gwamna Hyacinth Alia
Alia zai bunkasa fannin noma a Benue
Ya sake jaddada sadaukarwar gwamnatinsa wajen haɓaka fannin noma na zamani kuma mai amfani ga kasuwanci, wanda ke da ikon samar da ayyukan yi, rage fatara, da kuma samar da ci gaban tattalin arziki.
Gwamna Alia ya kuma ce gwamnati za ta ƙarfafa shirye-shiryen sarrafa amfanin gona da ƙara musu daraja da nufin rage asarar da ake yi bayan girbi da kuma inganta hanyoyin samun kuɗaɗe na manoma, jaridar gazettengr ta kawo labarin.

Source: Facebook
Gwamna Alia ya karfafa gwiwar manoma
“Ga manomanmu masu ƙwazo, bari na tabbatar maku cewa gwamnatinku tana tsaye daram tare da ku. Muna mutunta sadaukarwarku, muna yaba wa gudunmawarku, kuma muna ci gaba da kasancewa masu sadaukarwa wajen samar da yanayi mai kyau wanda za ku iya bunƙasa a cikinsa.”
“Ina ƙarfafa ku da ku yi amfani da kayan noman da ake samarwa a ƙarkashin wannan shiri. Ina kuma umartarku da ku ba da haɗin gwiwa ga hukumomin da abin ya shafa, sannan ku bi ƙa'idodin da aka kafa daki-daki domin tabbatar da nasarar wannan aiki."
- Gwamna Hyacinth Alia
Gwamna Alia ya samu tikitin APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2027 da ke tafe.
Gwamna Alia ya zama dan takarar ne bayan ya samu nasara a zaben fitar da gwanin da jam'iyyar APC ta gudanar a jihar Benue.
Sakamakon zaɓen kato bayan kato da aka sanar ya nuna cewa Alia ya samu ƙuri’u 367,786, inda ya doke abokan takararsa Jeffrey Kuranun da Terwase Orbunde, waɗanda suka samu ƙuri’u 2,923 da 3,247.
Asali: Legit.ng

