"Asiri Zai Tonu," Ana Zargin ba tsakani da Allah Kwankwaso Ya Hada Kai da Peter Obi ba
- Babban malamin coci a Najeriya, Fasto Elijah Ayodele ya ja hankalin Peter Obi kan alakarsa da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso
- Ayodele ya yi ikirarin cewa Kwankwaso ya hada kai da tsohon gwamnan jihar Anambra ne domin cimma burinsa na kashin kai
- Ya kuma gargadi Peter Obi kan yadda yake gudanar da harkokinsa na siyasa ba tare da nazari da lura da abubuwan da ke faruwa a kusa da shi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jagoran cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Fasto Elijah Ayodele, ya gargadi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, kan alakarsa da Rabiu Kwankwaso.
Ayodele ya bayyana cewa Peter Obi yana tsananin sha'awar cimma burinsa na mulkin Najeriya har ya kasa lura da wasu abubuwan da ke faruwa a kusa da shi da za su iya kawo masa cikas.

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta ruwaito cewa malamin addinin ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin, ya sanya wa hannu, .
Ayodele ya hango matsala ga Obi
Limamin cocin ya yi zargin cewa tsohon gwamnan jihar Anambra ba ya sauraron shawarwari ko umarnin Ubangiji, lamarin da ya sanya shi fadawa hannun mutanen da ba za su taimaka masa wajen cimma burinsa ba.
Ayodele ya ce:
"Peter Obi ba ya sauraron umarnin Ubangiji, kuma saboda haka ne ya fada hannun mutanen da ba su dace da burinsa ba.
"Kwankwaso ba zai yi wa Obi gwagwarmaya da zuciya daya ba. A karshe zai juya masa baya, amma har yanzu bai fahimci hakan ba. Tuni ya fara kawo rudani a tafiyar Obi na zama shugaban kasa."
Abin da ake zargin Kwankwaso na nema
Fasto Ayodele ya kara da cewa duk abin da Kwankwaso ke yi a halin yanzu yana da nasaba ne da bukatunsa na siyasa, ba wai domin tallafa wa Obi ba.
A cewarsa:
"Kwankwaso yana yin duk abin da yake yi ne domin amfanin kansa. Ina fata idanun Obi za su bude ya fahimci abin da ke faruwa a kusa da shi, amma har yanzu bai gani ba.
"Ba na kin Peter Obi, ina son sa kuma ina yaba masa saboda jarumtarsa, amma ban@ ganin ya kai matsayin da zai iya rike kujerar shugaban kasa ba."

Source: Twitter
Asirin Kwankwaso zai tonu
Har ila yau, Fasto Ayodele ya yi ikirarin cewa nan gaba kadan za a gano hakikanin manufofin Kwankwaso, kamar yadda Daily Post ta rahoto.
"Duk da haka, nan ba da jimawa ba za a gano abin da Kwankwaso ke shiryawa. Amma zuwa lokacin Peter Obi ya makara, domin ya riga ya zurfafa cikin lamarin," in ji shim
Peter Obi ya shawarci matasan Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya shawarci matasan Najeriya yayin da ake tunkarar zaben 2027.

Kara karanta wannan
Shugaban Obidients ya tabo batun 'rusa' masallacin Peter Obi lokacin da yake gwamna
Peter Obi ya buƙaci matasan Najeriya da su yi watsi da rarrabuwar kawuna ta ƙabilanci da addini, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai da makomar ƙasa.
Obi ya ce wasu ‘yan siyasa kan koma amfani da ƙabila, addini da batutuwan asali idan ba za su iya yin gogayya da sauran yan takara.
Asali: Legit.ng

