PDP Ta Kara Birkicewa, 'Yan Majalisa 4 na Jam'iyyar daga Bauchi Sun Koma APM
- Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta gamu da gagarumin koma baya yayin da wasu 'yan majalisar wakilai suka fice daga cikinta zuwa APM
- 'Yan majalisar wakilan wadanda suka fito daga jihar Bauchi sun sanar da ficewarsu daga jam'iyyar ne a hukumance a ranar Alhamis, 4 ga watan Yunin 2026
- Hakazalika, wani dan majalisar wakilai da ya fito daga jihar Nasarawa, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa SDP mai adawa a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Guguwar sauya sheka da ke kadawa a Majalisar Wakilai ta ƙara tsananta, yayin da 'yan majalisa huɗu daga jihar Bauchi suka ficewa jam'iyyar PDP zuwa APM.
Ficewarsu na zama matsayin wata sabuwar alama ta sauye-sauyen ƙawancen siyasa gabannin babban zaɓen shekarar 2027.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce an sanar da sauya shekar ne a hukumance ta hannun shugaban Majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, a ranar Alhamis, 4 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan
Atiku ya zayyano kurakuran gwamnatin Tinubu kan rashin tsaro "ta ki daukar darasi"
An karanta wasikun masu ficewa daga PDP
Tajudeen Abbas ya karanta wasiƙun 'yan majalisar da abin ya shafa dake sanar da majalisar shawararsu ta barin jam'iyyar PDP, TVC News ta kawo labarin.f
'Yan majalisar su ne Muhammad Shehu, mai wakiltar Mazabar Zaki, Aliyu Garu, mai wakiltar Mazabar Bauchi, Sani Tanko, mai wakiltar Mazabar Shira/Giade da kuma Mansur Soro, mai wakiltar Mazabar Darazo/Ganjuwa.
Dan majalisa ya bar APC zuwa SDP
Haka kuma, Jeremiah Umaru, wanda ke wakiltar Mazabar Akwanga/Nasarawa Eggon/Wamba ta jihar Nasarawa, shi ma ya sauya sheka.
Jeremiah Umaru ya sauya sheka ne daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa jam'iyyar SDP mai adawa a Najeriya.
Meyasa 'yan majalisa suka bar PDP?
Babban abin da suka kafa hujja shi a cikin wasiƙun sauya shekar tasu shi ne “rikice-rikicen cikin gida na jam'iyya” da kuma “Bukatar samar da kyakkyawan wakilci” ga al'ummomin mazabar da suke wakilta daban-daban.
Ficewar ta 'yan majalisar Bauchi guda huɗu tana da gagarumin muhimmanci duba da tasirin jam'iyyar PDP a jihar.

Source: Facebook
Sauya shekar ta ranar Alhamis ta biyo bayan jerin sauya sheka da aka gani a Majalisar cikin makon da ya gabata.
A ranar Talata, 'yan majalisa takwai suka sanar da ficewarsu daga PDP zuwa APM, yayin da wasu guda uku suka fice daga APC zuwa PDP da jam'iyyar NDC.
PDP ta tsaida dan takarar gwamna
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, ta tsayar da tsohon Ministan kwadago da samar da ayyuka, Sanata Joel Ikenya, a matsayin dan takararta na gwamna a Taraba bayan zaben fitar da gwani.
Sanata Joel Ikenya ya zama wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani na gwamna da ɓangaren jam'iyyar PDP karkashin jagorancin Turaki ya gudanar a Taraba.
Shugaban kwamitin zaɓen, Honorabul Felix Hassan Hyat, ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci, tare da yabawa kwamitin gudanarwar PDP na Taraba kan yadda aka gudanar da shi cikin lumana.
Asali: Legit.ng
