Sojoji Sun Samu Nasara kan 'Yan Ta'adda, an Kashe Tsageru da Ceto Mutanen da Aka Sace
- Dakarun sojojin Najeriya sun hana 'yan ta'adda sakat a yankin Gabas ta Tsakiya yayin da suka samu gagarumar nasara
- Sojojin na rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama bayan da suka kai masu farmaki
- Hakazalika, sojojin sun samu nasarar cewa wasu daga cikin mutanen da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a kauyen Ngoshe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Dakarun sojoji na rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas wato Operation Hadin Kai, a ƙarkashin aikin Operation Desert Sanity V/Siege Operation, sun samu nasara kan 'yan ta'adda.
Dakarun sojojin sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda da dama tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a yankin Arewa maso Gabas.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in yaɗa labarai na rundunar Operation Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar a ranar Alhamis, 4 ga watan Yunin 2026 a shafin X.
Sojoji sun ceto mutanen da aka sace
Laftanar Kanal Sani Uba ya bayyana cewa ayyukan dakarun sojojin sun kai ga ceto fararen hula da aka sace, kashe 'yan ta'adda, da kuma ƙaruwar mika wuya na mambobin iyalan 'yan ta'addan.
“A cikin wata babbar nasara, dakarun OPHK, yayin da suke gudanar da ayyukan farmaki a babban yankin Amuda, sun yi nasarar tarewa tare da ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su daga kauyensu na Ngoshe."
“Waɗanda abin ya shafa, waɗanda aka gano sunayensu a matsayin Malama Maryam Muhammad (shekara 20) da jaririnta namiji, Bello Muhammad (shekara 1 da watanni 4), suna cikin waɗanda aka sace a lokacin harin ta'addanci da aka kai a Ngoshe ranar 3 ga Maris, 2026.”
- Laftanar Kanar Sani Uba
'Yan yi wa 'yan ta'adda ruwan wuta
Ya ce an tsare waɗanda abin ya shafan ne a wata maboyar 'yan ta'adda da ke cikin tsaunin duwatsu na Mandara kafin su yi nasarar tserewa sakamakon tsananin hare-hare da aka kai a maboyar 'yan ta'addan, wanda hakan ya tilasta wa masu garkuwan barin su.

Kara karanta wannan
Atiku ya zayyano kurakuran gwamnatin Tinubu kan rashin tsaro "ta ki daukar darasi"

Source: Original
Jami'in hulda na jama'an na rundunar Operation Hadin Kai ya bayyana cewa bayan gudanar da binciken lafiya na farko, an sake haɗa waɗanda aka ceton lafiya tare da mambobin iyalansu ta hanyar shugabancin al'ummar Ngoshe.
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta bayyana cewa an kashe mayaƙan kungiyar ta'addanci ta ISIS 175 a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya.
Ta bayyana cewa an murkushe yan ta'addan ne a hare-haren hadin gwiwa da sojojin Najeriya da na Amurka suka gudanar a wani bangare na yaki da ta'addanci.
An lalata wuraren binciken ‘yan ta’addan, ma’ajiyar makamai, cibiyoyin kayan aiki, kayan yaki da hanyoyin samun kudaden da suke amfani da su wajen kai hare-hare.
Asali: Legit.ng
