Iran Ta Gargadi Saudiyya bayan Kulla Yarjejeniyar Tsaro da Pakistan, Turkiyya
- Dan majalisar Iran, Ebrahim Rezaei, ya ce yarjejeniyar tsaro da Pakistan da Turkiyya ba za ta tabbatar wa Saudiya da tsaro ba
- Ebrahim Rezaei ya bukaci mahukunta a Riyadh kan sauya manufofin kasar maimakon neman kariya daga wasu kasashe
- Turkiyya da Pakistan sun ce yarjejeniyar da aka kulla ba ta nufi wata kasa ba, illa karfafa tsaro da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Tehran – Dan majalisar dokokin Iran, Ebrahim Rezaei, ya ja kunnen Saudiyya kan yarjejeniyar tsaro da ta kulla da Pakistan da Turkiyya.
Dan majalisar ya garargadi kasar Saudiyya cewa yarjejeniyar tsaro da ta kulla da Pakistan da Turkiyya ba za ta samar mata da tsaron da take nema ba.

Source: Getty Images
Rezaei, wanda kuma mamba ne a kwamitin tsaro na kasa da harkokin wajen majalisar Iran, ya bayyana hakan a wani rubuta a shafinsa na X.
Me dan majalisar Iran ya gayawa Saudiyya?
Dan majalisar ya bayyana cewa ya kamata masarautar Saudiyya ta sauya manufofinta kan bangaren tsaro.
A cewarsa:
"Ya kamata Saudiyya ta sani cewa yarjejeniyar takarda da Turkiyya da Pakistan ba za ta ba ta tsaro ba, kamar yadda shekaru na dogaro da Amurka bangare guda bai samar mata da tsaro ba."
Ya kara da cewa:
"Ku gyara manufofinku domin kada ku rika rokon wasu su ba ku tsaro."
Turkiyya ta ce yarjejeniyar ba ta nufi wata kasa ba
A wani sako da ya wallafa a shafin X, daraktan sadarwa na fadar shugaban kasar Turkiyya, Burhanettin Duran, ya bayyana cewa yarjejeniyar Makka ba ta nufi wata kasa ta musamman ba.
Ya ce yarjejeniyar za ta karfafa hadin gwiwar tsaro da kuma karfin dakile barazana tsakanin Saudiyya, Pakistan da Turkiyya.
A cewarsa, hakan zai taimaka matuka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Kasashen uku sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro
Ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta bayyana cewa Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya, Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud, shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, da firaministan Pakistan, Muhammad Shehbaz Sharif, sun gudanar da taron koli kan tsaro a birnin Makka.
Sanarwar ta ce shugabannin sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro da ta ginu kan dadaddiyar alakar kasashen uku, dankon 'yan uwantaka da hadin kan Musulunci, tare da muradun tsaro da hadin gwiwar soja da suka dade suna yi.
Sanarwar ta kara da cewa yarjejeniyar tana nuna kudurin kasashen uku na kara karfafa tsaronsu tare da inganta zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a yankin da ma sauran sassan duniya domin samar da makoma mai tsaro da wadata.
Haka kuma, ta jaddada cewa an tsara yarjejeniyar ne domin karfafa hadin gwiwar dakile duk wani hari, inda ta tanadi cewa duk wani hari da aka kai wa daya daga cikin kasashen uku za a dauke shi a matsayin hari da aka kai musu baki daya.

Source: Getty Images
Maganar kawo karshen yaki da Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa - Donald Trump, shugaban ƙasar Amurka, ya yi magana kan lokacin da yake ganin za a kawo karshen yaki da Iran.
Shugaba Trump na Amurka ya bayyana cewa yana ganin yakin da ake yi da Iran zai ƙare "nan ba da jimawa ba."
Asali: Legit.ng


