An Matsawa Shugaban EFCC Lamba Ya Sauka ko Tinubu Ya Kore Shi

An Matsawa Shugaban EFCC Lamba Ya Sauka ko Tinubu Ya Kore Shi

  • Jam'iyyun adawa da wasu 'yan Najeriya sun buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya cire Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, bayan daskarar da asusun gwamnatin Osun
  • Masu sukar matakin sun zargi hukumar da nuna bangaranci a daidai lokacin da ake tunkarar zaɓen gwamnan Osun na ranar 15 ga Agusta
  • EFCC ta ce ta daskarar da asusun ne saboda zargin wasu mu'amaloli masu cike da shakku, amma Tinubu ya umarci a buɗe asusun, yana mai bayyana matakin a matsayin abin kunya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Osun – Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, Ola Olukoyede, na fuskantar matsin lamba da kiraye-kirayen ya yi murabus bayan rikicin da ya biyo bayan daskarar da asusun gwamnatin jihar Osun.

Jam'iyyun adawa da wasu 'yan Najeriya sun zargi hukumar da yin amfani da matakin ne saboda dalilan siyasa, musamman ganin cewa zaɓen gwamnan jihar zai gudana a ranar 15 ga Agusta.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya ballo ruwa, an bukaci ya yi murabus daga mukaminsa

Ola Olukoyede a wajen taro
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede. Hoto: EFCC Nigeria
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa jam'iyyar Accord da NNPP na daga cikin waɗanda suka buƙaci Olukoyede ya yi murabus, yayin da suka kuma yi kira ga Tinubu da ya kore shi idan bai sauka da kansa ba.

Maganar rufe asusun Osun

EFCC ta bayar da umarnin rufe asusun gwamnatin jihar Osun da ke First Bank ranar Laraba, bisa zargin wasu mu'amaloli da ake ganin suna da shakku.

Hukumar ta ce tana binciken asusun tun watan Maris na 2026, kuma doka ta ba ta damar daskarar da asusu na tsawon sa'o'i 72 idan akwai ingantaccen zato na aikata laifi.

Sai dai a ranar Alhamis, Shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumar da ta buɗe asusun, inda ya bayyana matakin daskarar da shi a matsayin abin kunya.

Maganar jam'iyyar Accord

Shugaban jam'iyyar Accord na ƙasa, Maxwell Mgbudem, ya ce jam'iyyar ta rasa amincewa da jagorancin EFCC bisa zargin cewa matakin da hukumar ta ɗauka na siyasa ne.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya shiga tsaka mai wuya kan rufe asusun gwamnati da umarnin Tinubu

Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja, Mgbudem ya buƙaci Olukoyede ya yi murabus, yana mai cewa matakin ya jefa hukumar da gwamnatin ƙasar cikin abin kunya.

Ya ce idan shugaban EFCC ya ƙi yin murabus, ya kamata Tinubu ya kore shi domin dawo da martabar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a wajen taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Martanin NNPP da 'yan Najeriya

Shugaban NNPP na ƙasa, Major Agbo, shi ma ya goyi bayan kiraye-kirayen Olukoyede ya yi murabus, ko da yake ya nuna damuwa kan yadda umarnin shugaban ƙasa na buɗe asusun zai iya shafar 'yancin EFCC.

Wasu 'yan Najeriya da suka yi tsokaci a kafar sada zumunta ta X sun kuma buƙaci Olukoyede ya sauka daga mukaminsa, inda wasu ke zargin hukumar da aiki da muradun jam'iyyar APC.

Sai dai wasu daga cikin masu magana kan batun sun ce ya kamata a bar EFCC ta kammala bincikenta ba tare da katsalandan ba, domin tabbatar da 'yancin hukumar wajen gudanar da ayyukanta.

An tura jami'an ICPC Osun

A wani labarin, mun ruwaito cewa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta ce za ta tura jami'anta zuwa dukkan ƙananan hukumomi 30 na jihar Osun yayin zaɓen gwamna da za a gudanar ranar 15 ga Agusta.

Kara karanta wannan

An yi walƙiya: ADC ta nemi Tinubu ya yi wa El Rufa'i yadda aka yi wa gwamnatin Osun

Kwamishinan ICPC mai kula da yaƙi da cin hanci a Osun, Yusuf Olatunji, ya bayyana hakan yayin wani gangamin wayar da kan jama'a kan illar sayen ƙuri'u a Osogbo.

Gangamin ya haɗa da jami'an hukumar, ma'aikatan INEC da 'yan bautar ƙasa, inda aka raba wa jama'a takardu masu ɗauke da bayanai kan illolin saye da sayar da ƙuri'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng