Tirkashi: Iran Ta Sake Kunyata Trump a Idon Duniya
- Kamfanin dillancin labarai na Mehr ya ce ikirarin Donald Trump na cewa Iran ta nemi Amurka kada ta sake kai mata hari karya ne
- Jami’an sojin Iran sun ce dakarunsu na cikin shirin ko-ta-kwana kuma a shirye suke su fuskanci duk wani yanayi
- Iran ta ce mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a rufe muddin Amurka ba ta daina abin da Tehran ta kira ayyukan ta'addanci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Iran - Iran ta musanta ikirarin shugaban Amurka, Donald Trump, cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nemi Amurka kada ta sake kai mata sabon hari.
Kamfanin dillancin labaran Mehr ya ambato wasu jami’an soja suna cewa wannan ikirari “sabuwar karya ce kawai,”.

Source: Getty Images
Tashar Press tv ta ce kamfanin dillancin labaran ya jaddada cewa rundunar sojin Iran na cikin shirin ko-ta-kwana kuma a shirye take domin fuskantar duk wani yanayi.
A ranar Asabar, Trump ya ce Amurka ta “shirya kai hari kan Jamhuriyar Musulunci,” amma Tehran da wasu kasashen Gabas ta Tsakiya sun roke shi da ya dakatar da kai sababbin hare-hare.
Shugaban kasar na Amurka ya ce ya yanke wannan hukunci ne bisa sharadin cewa za a cimma yarjejeniya da Iran.
Trump ya rubuta a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa:
“Wannan zai hada da bude mashigar Hormuz nan take, baki daya kuma gaba daya, tare da kawo karshen barazanar nukiliyar Iran.”
Iran ta yi matsaya kan Hormuz
A ranar Lahadi, kamfanin dillancin labarai na Fars ya ambato wata majiya da ke kusa da masu tattaunawa na Iran tana cewa:
“Muddin Amurka ta ci gaba da ayyukanta na kai hare-hare, mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a rufe.”
Iran ta toshe mashigar Hormuz tun bayan fara yakin, inda ta sanya sharadin cewa jiragen ruwa su nemi izini tare da biyan kudin wucewa kafin amfani da hanyar ruwan.
Sojoji sun musanta ikirarin
A cewar Fars, wata majiya daga bangaren soja ma ta yi watsi da ikirarin, tana mai cewa babu wani tushe da ya tabbatar da shi.
An ambato majiyar tana cewa:
“Muddin ayyukan adawa da mugayen matakan Amurka suka ci gaba, mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a rufe.”
“Wucewa za ta yiwu ne kawai ta hanyar da aka ware, bayan an hada kai da rundunar sojojin ruwa ta Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), sannan an samu izinin ketare mashigar Hormuz. Idan ba haka ba, sauran hanyoyin ba su da tsaro, kuma jiragen ruwa da suka yi yunkurin amfani da su za su fuskanci matsaloli.”

Source: Getty Images
Majiyar ta kuma jaddada cewa rahotannin da ke cewa Iran ta amince da wani tsari na sake bude mashigar Hormuz “ba su da tushe.”
Ta ce ba a yanke wani sabon hukunci ba, kuma ba a sauya wata manufa dangane da wannan muhimmiyar hanyar ruwa ba.
Maganar Trump kan kai wa Iran hare-hare
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ce Washington za ta ci gaba da kai wa Iran hare-hare masu tsanani.
Shugaba Trump ya kuma yi ikirarin cewa Iran ta rasa karfinta, inda ya ce ba ta da rundunonin sojojin kasa, ruwa da na sama.
Asali: Legit.ng


