Iran Ta Yi Martani bayan Trump Ya Nuna Son Ganawa da Mojtaba Khamenei

Iran Ta Yi Martani bayan Trump Ya Nuna Son Ganawa da Mojtaba Khamenei

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya nuna yiwuwar son ganawa jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei
  • Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi martani kan yiwuwar haduwar Mojtaba Khamenei da shugaban kasar na Amurka
  • Abbas Araghchi ya kuma bayyana dalilin da ya sanya ba a ganin Mojtaba Khamenei a bainar jama'a tun bayan nadin da aka yi masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi magana kan yiwuwar haduwa tsakanin Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka.

Abbas Araghchi ya yi watsi da batun yiwuwar haɗuwar Mojtaba Khamenei da Donald Trump, bayan da shugaban na Amurka ya buɗe kofar hakan.

An yi maganar haduwar Trump da Mojtaba Khamenei
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da Mojtaba Khamenei Hoto: Andrew Caballero-Reynolds, Reza B
Source: Getty Images

Jaridar Arab News ta ce Abbas Araghchi ya bayyana hakan ne a waga hira da ya yi da kafafen yaɗa labarai na Lebanon da aka gudanar a daren ranar Alhamis, 4 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

"Asiri zai tonu," Ana zargin ba tsakani da Allah Kwankwaso ya hada kai da Peter Obi ba

Trump ya bayyana cewa ya bayyana cewa yana son haduwa da Mojtaba Khamenei inda ya kara da cewa watakila za su iya haduwa a wani lokaci.

Me Iran ta ce kan haduwar Khamenei, Trump?

Abbas Aragchi ya rage muhimmancin yiwuwar hakan inda ya bayyana cewa haduwar ba abu ne mai yiwuwa a aikace ba.

“Na ga wani rahoto wanda a fili ya nuna cewa shi (Trump) ya bayyana cewa a shirye yake don gudanar da taro ko kuma yana son gudanar da taro."
"Ina jin ya kamata mu kasance masu fuskantar gaskiya kuma mu yi tunani a cikin ainihin duniyar da muke ciki."

- Abbas Araghchi

An naɗa Ayatollah Mojtaba Khamenei a matsayin babban jagoran Iran a watan Maris bayan mutuwar mahaifinsa, Ali Khamenei, a cikin hare-haren hadin gwiwa na Amurka da Isra'ila a ranar 28 ga watan Fabrairu.

Araghchi ya sha da kyar a harin Amurka

Araghchi ya bayyana a cikin hirar cewa a lokacin hare-haren da suka kashe Ali Khamenei, yana cikin ofishin jagoran, amma yana wani ɓangare daban na ginin, shi ya sa bai samu rauni ba, jaridar Economic Times ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Trump yana son ganawa da Mojtaba Khamenei na Iran

Hare-haren sun tunzura Iran wajen ɗaukar fansa ta hanyar harba makami masu linzami da hare-haren jiragen marasa matuka a kan Isra'ila da sansanonin sojojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

Araghchi ya sha da kyar a harin Amurka
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi Hoto: @Araghchi
Source: Twitter

Meyasa ba a ganin Mojtaba Khamenei?

Araghchi ya kuma ce sabon jagoran na Iran ana da cikakken kusanci da tasiri a cikin harkokin ƙasar kuma yana da cikakken iko.

Ya ce rashin fitowar Mojtaba Khamenei a idon jama'a tun bayan naɗinsa ya kasance “saboda dalilai ne na tsaro” da suka shafi yaƙin, wanda aka ɗakata da shi tun ranar 8 ga watan Afrilu sakamakon wata yarjejeniyar tsagaita wuta.

Mojtaba Khamenei ya yi gargadi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Mojtaba Khamenei, ya yi kira ga al'ummar ƙasar da su ƙarfafa haɗin kai tare da kauce wa duk wani abu da zai iya haddasa rabuwar kai a tsakanin jama'a.

Sabon jagoran addinin na Jamhuriyar Musulunci na Iran ya bayyana cewa maƙiyan kasar na ƙoƙarin cimma wasu manufofi ta hanyar tayar da rashin jituwa.

Khamenei ya jaddada cewa haɗin kai tsakanin jama'a shi ne babban abin da zai taimaka wa Iran wajen tunkarar duk wata barazana daga maƙiyanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng