Trump Ya Harzuka da Majalisa Ta Umurci a Janye Sojojin Amurka a Yaki da Iran
- Majalisar wakilan Amurka ta kada kuri'ar amincewa da kudirin da ke neman tilastawa Shugaba Donald Trump janye sojojin kasar daga yaki da Iran
- Shugaba Donald Trump ya soki kudirin inda ya nuna cewa ya zo a daidai lokacin da yake tsakiyar tattaunawa da Iran
- Trump ya caccaki 'yan jam'iyyar Democrat da suka kawo kudirin da kuma na Republican wadanda suka goya masu baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya soki wata ƙuri'ar da aka kaɗa a Majalisar wakilan Amurka da ke neman ba da umarnin janye dakarun sojojin kasar daga yaƙin Iran.
Trump ya bayyana kada kuri'ar a matsayin wani mataki na “rashin kishin ƙasa” wanda ya kawo cikas ga tattaunawar da ake yi da birnin Tehran.

Source: Getty Images
Trump ya bayyana hakan ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Alhamis, 4 ga watan Yunin 2026.
Me Trump ya ce kan majalisa?
"Wannan ƙuri'ar da galibi ta kasance ta alama ce kawai ta zo ne daidai a tsakiyar tattaunawata ta ƙarshe ta kawo ƙarshen yaƙi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran."
“Wane ne zai yi irin wannan abu na rashin kishin ƙasa. Sun san inda tattaunawar ta tsaya.”
- Donald Trump
Majalisa ta kawo cikas ga Trump
A cikin wani babban kalubale ga Trump, mambobi huɗu na jam'iyyarsa ta Republican mai rinjaye sun haɗa gwiwa da 'yan jam'iyyar Democrat wajen marawa matakin baya, wanda ya tsallake da ƙuri'u 215-208, kuma a yanzu haka ya nufi Majalisar Dattawa.
Wannan mataki, wanda daga ƙarshe zai fuskanci kin amincewa daga shugaban ƙasa, ya kasance karo na farko da Majalisar Wakilai da Republican ke iko da ita ta amince da wani mataki da ke neman tilasta wa Trump dakatar da ayyukan soja a kan Tehran tun lokacin da yaƙin ya ɓalle watanni uku da suka gabata.
'Yan jam'iyyar Democrat suna zargin Trump da keta tsarin mulki ta hanyar ƙaddamar da hare-hare a kan Iran tare da Isra'ila a ƙarshen watan Fabrairu ba tare da amincewar majalisa ba.

Kara karanta wannan
Netanyahu ya yi magana kan takaddamarsa da Trump, ya fadi halin da alakarsu ke ciki

Source: Facebook
A ƙarkashin dokar ikon yaƙi shugabannin ƙasa suna da kwanaki 60 na samun amincewar majalisa bayan sun tura dakarun Amurka cikin rikici.
Wannan wa'adi ya cika makonni da suka gabata, kuma 'yan jam'iyyar Democrat sun ce Trump yana karya doka a yanzu.
Trump ya soki 'yan majalisar Amurka
“'Yan jam'iyyar Democrat sun gwammace su ga kasarmu ta gaza maimakon su ba ni wata nasarar, cikin nasarori da dama."
“Mambobin Republican guda huɗu kuwa, wannan wani labari ne na daban, sun cika son nuna kai! Ya kamata su ji kunyar kansu."
- Donald Trump
Trump na son ganawa da Mojtaba Khamenei
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan tattaunawa da Mojtaba Khamenei na Iran.
Shugaba Trump na Amurka ya ce yana sa ran zai gana da jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, kuma suna fahimtar juna sosai.
Donald Trump ya dade yana nuna goyon baya ga ganawa kai tsaye da shugabannin ƙasashen da Amurka ke saɓani da su.
Asali: Legit.ng
