Hilda Dokubo: Jarumar Fim Ta Yi Wa Shugaba Tinubu Tatas kan Matsalar Rashin Tsaro
- Ana ci gaba da kokawa kan matsalar rashin tsaron da ta addabi sassa daban-daban na Najeriya wadda ta jawo asarar rayuka
- Jarumar fina-finan masana'antar Nollywood, Hilda Dokubo, ta soki Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan matsalar rashin tsaro
- Hilda Dokubo ta nuna cewa yayin shugaban kasar da mukarraban gwamnati ke samun cikakkan tsaro, an bar talakawa na shan wahalhalu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Rivers - Fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Hilda Dokubo, ta mayar da martani ga kalaman Shugaba Tinubu a kan sha'anin rashin tsaro.
Hilda Dokubo ta soki shugaban kasar kan yadda al'amuran tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a kasar nan.

Source: Instagram
Jarumar fim din ta yi kalaman ne a cikin wani bidiyo da ta sanya a shafinta na Facebook a ranar Alhamis, 4 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Katsina ta yi magana kan sace Janar da matarsa, ta fadi kokarin da take yi
Hilda Dokubo ta soki Shugaba Bola Tinubu
Hilda Dokubo ta nuna baƙin ciki game da ƙaruwar garkuwa da mutane da hare-hare na tashe-tashen hankula a faɗin ƙasar.
Yayin da take kiran gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa tare da nuna juyayi, ta soki shugaban ƙasar da cewa ya ware kansa daga wahalhalun da 'yan ƙasa ke ciki.
Hilda ta shaida wa shugaban ƙasar cewa 'yan Najeriya ba sa neman darussa daga littafin mai tsarki, misalai, ko huɗubobi, illa dai amsoshin dalilin da ya sa garkuwa da mutane, hare-hare, da fargaba suka ci gaba da mamaye rayuwar yau da kullum.
Jarumar fim ta koka kan sace yara
Ta nuna takaicin cewa har yanzu ana sace yara, ana kai samame a kauyuka, manoma suna barin gonakansu, kuma iyalai da dama suna alhinin rashin masoyansu da suka rasa rayukansu a cikin tashe-tashen hankula.
Ta bayyana yadda jami'an gwamnati ke more kyakkyawan tsaro yayin da talakawa 'yan Najeriya ke fuskantar wahalhalun rayuwa.

Kara karanta wannan
Majalisar dinkin duniya ta turo sako kan daliban da aka sace a jihohin Borno da Oyo
“Kuna rayuwa mai daɗi. Ku na tuƙi a cikin motocin da harsashi bai ratsa su tare da rakiyar jami'an tsaro sanye da makamai a ɓangarori biyu. Ofishinku yana da ƙofar da harsashi bai huda ta da kuma dogayen jerin gwano na jami'an tsaro kafin a iya ganinku."
“Amma ba mu talakawan Najeriya ba, saboda haka ba kwa jin raɗadinmu, kuma shi ya sa kuke iya nisanta kanku da kukanmu ta hanyar kawo misalin Abraham and Isaac."
- Hilda Dokubo

Source: Facebook
Rashin tsaro na sosa zuciyar Hilda Dokubo
Ta bayyana sace yara 'yan makaranta a matsayin abin sosa zuciya, sannan kuma ta nuna baƙin ciki game da fargabar da iyayen yaran da aka yi garkuwa da su ke fuskanta.
Tsohuwar jarumar ta jaddada cewa ta fi damuwa da ko gwamnati za ta iya kare rayuka da dukiyoyi yadda ya kamata, inda ta ƙara da cewa wannan ita ce tambayar da 'yan Najeriya da dama ke son a ba su amsa.
Ya kamata a gaya masa gaskiya
Ibrahim Kabir ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a fito a gayawa Shugaba Tinubu gaksiya kan matsalar rashin tsaro.
"Abubuwa kullum suna kara tabarbarewa, kashe-kashe sun yi yawa, an hana mutane sakat, gwamnati kullum sai alkawari take yi amma ta kasa cikawa."

Kara karanta wannan
Hashim: Dan takarar shugaban ƙasa ya faɗi yadda zai raguzo da farashin Dala idan ya ci zabe
"Lokaci ya yi da za a gaya masa gaskiya, idan ba zai iya ba ya koma gefe. Da kasashen da aka san darajar rai da tuni shugaban kasa ya yi murabus.*
- Ibrahim Kabir
'Yan bindiga sun kori mutane a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu tsagerun 'yan bindiga dauke da makamai sun addabi mutanen jihar Sokoto da hare-hare.
Aƙalla mutanen da ke rayuwa a kauyuka 15 ne suka tsere suka bar gidajensu biyo bayan hare-haren haɗin gwiwa da 'yan bindiga suke kai wa.
'Yan bindigan sun kai hare-haren ne tsakanin kwanaki hudu a ƙaramar hukumar Tureta da ta Sabon Birni da ke jihar Sokoto.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng