Babban Basarake a Kebbi Ya Samo Mafita ga Mutanensa kan Matsalar 'Yan Bindiga

Babban Basarake a Kebbi Ya Samo Mafita ga Mutanensa kan Matsalar 'Yan Bindiga

  • Mai martaba Sarkin Argungu a jihar Kebbi ya yi kira da babbar murya ga mutanensa kan matsalar hare-haren 'yan bindiga
  • Alhaji Muhammad Samaila Mera ya bukaci mutane da su hada karfi da karfe wajen mallakar makamai domin kare kansu
  • Babban basaraken ya bayyana cewa baya goyon bayan mutane su dauki doka a hannunsu ta hanyar farmakar sauran kabilu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Mai martaba Sarkin Argungu, Alhaji Muhammad Samaila Mera, ya yi muhimmin kira ga jama'arsa kan matsalar 'yan bindiga.

Alhaji Muhammad Samaila Mera ya yi kira ga jama'arsa da su mallaki makamai ta hanyar da doka ta amince da ita, domin kare kauyukansu daga hare-haren 'yan bindiga saba kai musu akai-akai.

Sarkin Argungu ya ba da shawara kan matsalar 'yan bindiga
Mai martaba Sarkin Argungu, Alhaji Muhammad Samaila Mera Hoto: Yahaya Danjada
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin wani taro da ya gudanar da hakimai, dagatai, da kuma masu unguwanni a fadarsa da ke Argungu.

Kara karanta wannan

"An kashe bayin Allah"; Mutane sun bar kauyukansu a Sokoto sakamakon hare haren 'yan bindiga

Wace shawara Sarkin Argungu ya ba da?

Haka kuma, ya buƙaci kauyukan da ke cikin masarautar da su kasance cikin shiri kuma su ɗauki matakan riga-kafi a kan 'yan ta'adda, tashar DW Hausa ta kawo labarin.

Ya ƙara da cewa ya kamata garuruwa su duba yiwuwar tara kuɗaɗe domin sayan makamai waɗanda doka ta amince da su domin kare kansu.

“Idan ku ka mallaki irin waɗannan makamai bisa doka, ku tabbatar 'yan bindigan sun san cewa garuwanku suna da hanyoyin kare kansu. Wannan kaɗai zai iya zama abin tsoratarwa kuma ya hana kai hare-hare."

- Alhaji Muhammad Samaila Mera

Kara karanta wannan

Atiku ya zayyano kurakuran gwamnatin Tinubu kan rashin tsaro "ta ki daukar darasi"

Sarki ya bukaci jama'a su kare kansu

Sarkin ya jaddada cewa addinin Musulunci ba ya ƙarfafa mutane su kasance cikin rashin katabus, a lokacin da ake fuskantar tashe-tashen hankula.

“Ba daidai ba ne ga musulmi ya kasance kara-zube yayin da 'yan bindiga ke kashe mutane, sace mutane, da kuma yi wa mata fyade. Ku kasance cikin shiri domin kare kanku, iyalanku, da garuruwanku daga kowane hari."

- Alhaji Muhammad Samaila Mera

Babban basaraken ya nuna baƙin ciki cewa al'ummomi da dama sun zama masu rauni saboda ba su da hanyoyin kare kansu.

“Idan bindiga suka kawo hari, mutane suna fara guduwa, har da shugabannin ƙauyuka. Wannan yana faruwa ne saboda al'ummomi ba su da isassun hanyoyin kare kansu.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace tsohon shugaban APC, sun masa bidiyo yana neman agaji

- Alhaji Muhammad Samaila Mera

Sarkin Argungu ya ba da shawara kan rashin tsaro
Sarkin Argungu, Alhaji Muhammad Samaila Mera Hoto: Tsalha Baraya
Source: Facebook

Sarkin Argungu bai so a dauki doka a hannu

Ya bayyana cewa ba ya ƙarfafa gwiwar al'ummomi su ɗauki doka a hannunsu ko kuma su shiga cikin ayyukan ta'addanci, a'a, yana ba da shawara ne a kan kariya ta halal, inda ya lura cewa ƙalubalen tsaro ya zama mai tsanani da hukumomin tsaro kaɗai ba za su iya magance shi ba.

Basaraken ya ce abin baƙin ciki ne ga al'ummomi su ci gaba da rasa rayuka ba tare da wani nau'i na turjiya ba, yayin da ya yi gargaɗi game da tashe-tashen hankula na ƙabila da kisan gilla da ya wuce gona da iri.

Sarkin ya yi gargaɗin cewa ba zai tallafa wa duk wanda ke ɗauke da makamai domin ya kai hari ga sauran ƙabilu ba ko kuma ya shiga cikin kisa ba bisa doka ba.

'Dan majalisa ya yi magana kan rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ede ta Arewa/Ede ta Kudu/Egbedore/Ejigbo, Hon. Bamidele Salam ya yi maganganu kan matsalar rashin tsaro.

Kara karanta wannan

An yaudari yan Jigawa da jita jitar ba da tallafin rigakafin Covid 19

Ya ce shugabanni da dama suna yin watsi da matsalar rashin tsaro da ke ƙaruwa saboda ’ya’yansu suna zuwa makarantu masu zaman kansu ko kuma suna karatu a ƙasashen waje.

'Dan majalisar ya kafa hujja da cewa masu riƙe da muƙaman gwamnati da dama ba su jin raɗaɗin matsalolin da iyalai marasa ƙarfi ke fuskanta

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng