Satar Dalibai: Hanyoyi 6 da Makarantu Za Su Bi don Kare Kansu daga 'Yan Bindiga a Najeriya
- Hedkwatar tsaron Najeriya ta ja hankalin makarantu a fadin kasar nan kan muhimmancin daukar matakan kariya
- Hakan na zuwa ne bayan hare-haren da aka kai tare da garkuwa da dalibai da malamai da dama a jihohin Borno da Oyo
- Babbar hedkwatar sojojin Najeriya ta ba da shawarwari shida da take ganin za su taimaka wajen tabbatar da tsaron makarantu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hedikwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ) ta bukaci makarantu a fadin kasar nan su kara kaimi wajen daukar matakan kariya bayan hare-haren sace dalibai da suka faru a jihohin Oyo da Borno.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a, DHQ ta bayyana lamarin sace daliban a matsayin gargadi da ke nuna bukatar daukar karin matakan kariya a makarantu.

Source: Twitter
Ta kuma lissafo muhimman hanyoyi guda shida da za su taimaka wajen tabbatar da tsaron makarantu da dalibai a fadin kasar nan, kamar yadda Premium Times ta kawo.

Kara karanta wannan
Majalisa ta fara ɗaukar mataki kan rashin tsaro, ana son samar da yan sandan jihohi
Hanyoyi 6 na ba makarantu kariya
Sanarwar ta bukaci makarantu su karfafa tsarin tsaro na zahiri da na zamani ta hanyar gina katanga mai inganci, sanya na'urorin CCTV da sauran kayan sa ido da za su iya gano barazana tun kafin ta afku.
Haka kuma, ta shawarci makarantu da su hada kai da amintattun matasa daga al'ummomin da suke cikinsu domin taimakawa wajen kare dalibai da kadarorin makarantu.
DHQ ta ce ya zama dole makarantu su samar da cikakken tsarin tunkarar matsalolin gaggawa, tare da gudanar da sintirin tsaro akai-akai domin tabbatar da cewa malamai da dalibai sun san yadda za su tunkari duk wata barazana.
Sanarwar ta kuma bukaci a horas da shugabannin makarantu, malamai da sauran ma'aikata yadda za su gano abubuwan da ke nuna hadari, su kai rahoto cikin gaggawa tare da daukar matakin da ya dace.
DHQ ta jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin makarantu, iyaye, al'ummomi, jami'an tsaro da hukumomin tabbatar da doka domin gano barazana a kan lokaci da daukar matakin gaggawa idan wata matsala ta taso.
Har ila yau, ta bukaci a samar da hanyoyin sanya ido da bayar da rahoto cikin makarantu da al'ummomi, kamar yadda Punch ta rahoto.

Source: Twitter
Yadda za a taimaki jami'an tsaro
Sanarwar ta ce:
"Idan ka ga wani abu mai tayar da hankali, ka sanar. Kai rahoto cikin lokaci na iya taimakawa jami'an tsaro su dakile hare-hare kafin su afku."
Shawarwarin DHQ sun yi daidai da manufofin shirin Safe Schools Initiative da Gwamnatin Najeriya ta kaddamar a shekarar 2014 bayan sace dalibai mata 276 daga makarantar Chibok a jihar Borno.
Sojoji sun kashe manyan yaran Abu Mainok
An ji cewa dakarun sojojin Najeriya da na Amurka sun yi nasarar kashe wasu manyan kwamandojin kungiyar ISWAP uku a jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa wadanda sojojin suka kashe na cikin manyan yaran shugaban ISWAP, Abu-Bilal al-Minuki (Abu Mainok) wamda aka tura lahira kwanakin baya.
Majiyoyi sun bayyana cewa bayan wannan nasara, an kashe fitattun kwamandojin kungiyar yan ta'addan, ciki har da Abubakar Buduma, jagoran yankin Kirta Wulgo.
Asali: Legit.ng
