"An Kashe Bayin Allah"; Mutane Sun Bar Kauyukansu a Sokoto sakamakon Hare Haren 'Yan Bindiga
- 'Yan bindiga sun kai hare-hare a wasu kauyukan jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma na tarayyar Najeriya
- Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka mutane da dama tare da tilasta wa mazaunan kauyukan tserewa daga gidajensu
- Rundunar 'ya sandan jihar Sokoto ta bayyana cewa ta tura karin jami'ai zuwa kauyukan da lamarin ya shafa domin samar da tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Aƙalla mutanen kauyuka 15 ne suka tsere suka bar gidajensu biyo bayan hare-haren haɗin gwiwa da 'yan bindiga suka kai a Sokoto.
'Yan bindigan sun kai hare-haren ne tsakanin ranar Lahadi da Laraba a ƙaramar hukumar Tureta da ta Sabon Birni da ke jihar Sokoto.

Source: Twitter
Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa aƙalla mutane 52 ne aka kashe a hare-haren, ciki har da mutane 46 a kauyukan karamar hukumar Tureta da kuma wasu guda shida a karamar hukumar Sabon Birni.
'Yan bindiga sun yi barna a Sokoto
Daruruwan mazauna yankin sun rabu da muhallansu sannan aka lalata gidaje da dama sakamakon hare-haren.
Mazauna kauyen Dan Gulbi a karamar hukumar Tureta sun ce tashe-tashen hankulan sun fara ne a ranar Lahadi, 31 ga watan Mayun 2026 lokacin da 'yan bindiga sanye da muggan makamai suka farmaki yankin, inda suka kashe mutane tare da tilasta wa iyalai da dama tserewa.
An ce maharan sun dawo a ranar Talata, 2 ga watan Yunin 2026 inda suka kai sababbin hare-hare a Dan Gulbi, Dansanberu, Baga, Jandutsi da sauran maƙwabta, lamarin da ya jawo ƙarin asarar rayuka, ƙona gidaje, da kuma tilasta wa ƙarin mazauna yankin barin gidajensu.
Mutane sun gudu daga gidajensu
Wani mazaunin Dan Gulbi, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalidai na tsaro, ya bayyana cewa an kashe mutane fiye da 10 a ƙauyen, yayin da aka ruwaito cewa an kashe wasu mutane 10 a kauyen Dansanberu da ke kusa da su.
Ya ƙara da cewa an kashe mutane biyar a Baga, yayin da wasu mutane biyu suka rasa rayukansu a Jandutsi.
A cewarsa, hare-haren sun haifar da raba mutane da muhallansu a faɗin yankin yayin da mazauna garin suka bar gidajensu kuma suka nemi mafaka a wurare mafi aminci.
Wadanne kauyukan Sokoto abin ya shafa?
Ya lissafa kauyukan da aka kaurace masu a karamar hukumar Tureta da suka haɗa da Dan Gulbi, Dansanberu, Jandutsi, Baga, Barayar Giwa, Birisawa, Mallanje da kuma Ketare.
“Waɗannan ƙauyuka a takaice sun koma fanko. Mutane suna dawowa ne kawai na ɗan lokaci domin ɗaukar kayan abinci kafin su koma inda suke fakewa."
- Wata majiya
Majiyar ta ce mazauna yankunan da abin ya shafa da suka rasa muhallansu a halin yanzu suna fake ne a garin Tureta, Gummi, Gamo, Wawar Icce, Helhendu, Jabaka da kuma Goshe.

Source: Original
Kauyuka sun zama kango
Wani mazaunin garin ya ce kauyen Dan Gulbi kaɗai yana da yawan jama'a da ya fi 1,500, amma ƙasa da mutane 10 ne kawai suka rage a ƙauyen a halin yanzu.
Ya bayyana cewa:
“Ko waɗanda suka rage ɗin ba sa kwana a ƙauyen. Suna amfani da mafi yawan lokutansu wajen ɓuya a daji kuma suna dawowa ne kawai jefi-jefi."
Ya bayyana cewa fiye da mazauna 500 da suka rasa muhallansu daga Dan Gulbi a halin yanzu suna fakewa ne a garin Gummi da ke maƙwabtaka a jihar Zamfara.
'Yan sanda sun yi bayani
Yayin da aka tuntuɓe shi, Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya ce an tura dakarun haɗin gwiwa na 'yan sanda da na sojoji zuwa kauyukan da abin ya shafa a Tureta.
“Mun tura jami'an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa da sanyin safiyar ranar Alhamis. Sai dai kuma, har yanzu suna kan gudanar da aiki a daidai lokacin da muke magana, kuma ba mu riga mu samu cikakken rahoto daga gare su ba."
- DSP Ahmad Rufai
Ya ce zai tuntuɓi DPO na Sabon Birni domin samun sababbin bayanai game da kauyukan da suka rasa muhallansu a ƙaramar hukumar.
'Yan bindiga sun yi kashe rai a Abuja
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wani sashe na babban birnin tarayya Abuja.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan da ke dauke da makamai sun sace mutane tare da kashe wani dan banga da ke tsaron jama'a a yankin.
Maharan wadanda ke dauke da makamai sun kuma sace mutane huɗu a harin da suka kai yankin Byazhin da ke Kubwa, a ƙaramar hukumar Bwari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



