Mumnunan Rikicin Manoma da Makiyaya Ya Barke a Bauchi, Rayuka Sun Salwanta

Mumnunan Rikicin Manoma da Makiyaya Ya Barke a Bauchi, Rayuka Sun Salwanta

  • Wani rikici ya barke tsakanin manoma da makiyaya a jihar Bauchi wanda ya jawo asarar rayukan mutane tare da raunata wasu
  • An samu asarar rayukan mutane bakwai yayin da aka lalata gidaje masu yawa sakamakon barkewar rikicin
  • Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewa ta tura jami'an tsaro domin dawo da doka da oda a yankin da lamarin ya auku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - An samu asarar rayukan mutane bakwai, wasu guda shida sun raunata, sannan aka lalata gidaje da dama biyo bayan wani mummunan rikicin manoma da makiyaya a jihar Bauchi.

Rikicin ya ɓarke ranar Alhamis, 4 ga watan Yunin 2026 tsakanin manoma da makiyaya a kauyukan Lanzai da Dosho da ke karamar hukumar Darazo ta jihar Bauchi.

Makiyaya da manoma sun gwabza fada a Bauchi
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Source: UGC

Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da aukuwar lamarin ranar Alhamis, 4 ga watan Yunin 2026, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ya nuna.

Kara karanta wannan

Atiku ya zayyano kurakuran gwamnatin Tinubu kan rashin tsaro "ta ki daukar darasi"

Manoma da makiyaya sun yi rikici a Bauchi

Rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa jami'an tsaro sun dawo da doka da oda a kauyukan da mummunan rikicin ya shafa.

Jami'in yaɗa labarai na rundunar 'yan sandan, SP Nafiu Habib, ya ce rundunar ta sami rahoton neman ɗauki da misalin ƙarfe 9:20 na safe cewa wasu da ake zargi Fulani makiyaya ne sun kai wa manoma hari a lokacin da suke zuba takin gida a gonakansu da ke bayan gari a kauyen Lanzai.

Harin ya jawo martani na ramuwar gayya daga matasan Lanzai, waɗanda suka haɗu suka farmaki Dosho, wani mazaunin Fulani.

A lokacin ramuwar gayyar, an ƙona bukkoki kusan 50, sannan aka lalata kayayyakin amfanin gida da dama, jaridar The Punch ta kawo labarin.

“Lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai, yayin da wasu guda shida suka samu raunuka mabanbanta kuma suna karɓar magani a asibiti."

- Nafiu Habib

An kona gidajen makiyaya

Kakakin 'yan sandan ya ƙara da cewa an samu gagarumar asara wajen lalata gidajen zama da sauran kayayyakin amfani.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Yadda aka yi yunkurin tayar da bam a gidan gwamnatin Ondo

Ya ce biyo bayan tashe-tashen hankula, an tura dakarun 'yan sanda na musamman zuwa yankunan da abin ya shafa domin dawo da doka da oda, hana ƙarin bazuwar rikici, da kuma fara bincike.

Manoma da makiyaya sun yi rikici a Bauchi
Taswirar jihar Bauchi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kwamishinan 'yan Sanda, Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan musabbabi da kuma dalilan da suka jawo aukuwar wannan rikici.

Ya tabbatar wa mazauna yankin cewa za a gano waɗanda ke da alhakin kai harin farko da kuma rikicin ramuwar gayyar, sannan a gurfanar da su gaban shari'a.

Rikicin manoma da makiyaya ya barke a Taraba

A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla mutane 16 ne suka mutu sakamakon rikice-rikicen da suka ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a jihar Taraba.

Mummunan rikicin manoman da makiyayan ya ɓarke ne a ƙaramar hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba, inda aka zubar da jinin mutane.

Harin farko ya faru ne a ƙauyukan Mungadosso da Bandawa, inda ake zargin wasu makiyaya sun kai hare-hare uku a jere, suka kashe mutane 10, tare da ƙona gidaje da dama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng