Majalisar Dinkin Duniya Ta Turo Sako kan Daliban da Aka Sace a Jihohin Borno da Oyo

Majalisar Dinkin Duniya Ta Turo Sako kan Daliban da Aka Sace a Jihohin Borno da Oyo

  • Majalisar dinkin duniya ta nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ta fara ruguza aminci da tsaron da ake da shi a makarantu a Najeriya
  • Ta bukaci hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a Najeriya da su gaggauta yin duk mai yiwuwa wajen kubutar da daliban Oyo da Borno
  • Wannan na zuwa ne bayan wasu 'yan ta'adda sun shiga makarantu daban-daban a jihohin Oyo da Borno, inda suka sace dalibai da malamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babban jami’in kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) a Najeriya, Mohamed Malick Fall, ya yi magana kan daliban da 'yan bindiga suka sace a Oyo da Borno.

Wakilin Majalisar dinkin duniya ya yi kiran da a gaggauta sako ɗaliban makaranta da malaman da aka sace a hare-haren baya-bayan nan da aka kai a jihohin Oyo da Borno.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta yi ikirarin hallaka kwamandan Hezbollah ana kokarin tsagaita wuta a Lebanon

Mohamed Malick Fall.
Babban jami'in kula da harkokin jin kai na Majalisar dinkin duniya a Najeriya, Mohamed Malick Fall Hoto: @MohamedFall
Source: Twitter

Daily Trust ta ce Mohammed Fall ya yi wannan kiran ne bayan ya gana da wata tawaga daga Cibiyar Kula da Harkokin Kare Makarantu ta Ƙasa a Abuja, ƙarƙashin jagorancin Dr. Samuel Umanah.

Majalisar dinkin duniya ta nuna damuwa

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya nuna matsananciyar damuwa game da yadda rashin tsaro ke ƙara ta'azzara a makarantu da cibiyoyin ilimi a faɗin ƙasar nan.

Mohammed ya bayyana hare-haren a matsayin barazana ga ilimi da kuma kariya ga ƙananan yara, in ji rahoton Bussiness Day.

Taron ya sake duba ƙalubalen tsaro da makarantu ke fuskanta, sannan ya nuna juyayi da goyon baya ga iyalai, mahukuntan makarantu, da kuma al'ummomin da lamarin ya shafa.

Yadda aka sace dalibai a Oyo da Borno

A jihar Oyo, wasu 'yan bindiga sun kai hari a makarantu uku da ke ƙaramar hukumar Oriire, inda suka yi garkuwa da ɗalibai sama da 40 da malamai bakwai a ranar 15 ga Mayu, 2026.

Kara karanta wannan

Farashin danyen mai ya ruguzo bayan Trump ya hana Isra'ila kai hari Lebanon

Irin wannan harin ya faru a garin Mussa na jihar Borno, a nan 'yan Boko Haram/ISWAP suka shiga makarantu uku tare da yin garkuwa da yara sama da 40, waɗanda akasarinsu ke tsakanin shekaru biyu zuwa biyar.

Mohammed Fall ya bayyana garkuwa da mutanen a matsayin abin tada hankali ƙwarai, yana mai jaddada cewa ya kamata makarantu su kasance wurare masu aminci na neman ilimi.

"Dole ne makarantu su kasance matsuguni masu aminci don koyo, ba wuraren tsoro ba. Bai kamata kananan yara su zama abin farmaki ba," in ji shi.
Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana jawabi a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Majalisar ta aika sako ga jami'an tsaro

Wakilin Majalisar dinkin duniyan ya yi kira ga hukumomi da su ƙara nunka ƙoƙari wajen ganin an dawo da dukkan wadanda aka yi garkuwa da su lafiya, da kuma tabbatar da cewa an hukunta waɗanda ke da alhakin aikata hakan.

Haka zalika, ya jaddada aniyar Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da tallafawa samar da yanayin koyo mai aminci, haɗaka, da kuma kuɓuta daga tashe-tashen hankula.

Da gaske an sako daliban Oyo?

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin jihar Oyo ta ce bidiyon da ke yawo na cewa an sako dalibai da malamai da aka sace a Oriire karya ne.

Kara karanta wannan

Hashim: Dan takarar shugaban ƙasa ya faɗi yadda zai raguzo da farashin Dala idan ya ci zabe

A cikin wata sanarwa, Kwamishinan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama'a na jihar, Prince Dotun Oyelade, ya bayyana cewa rahoton da ke nuna an sako daliban ba gaskiya ba ne.

Ya ce gwamnatin jihar Oyo na ci gaba da gudanar da wasu tsare-tsaren sirri da hadin gwiwa da hukumomin tsaro domin tabbatar da an kubutar da su cikin koshin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262