Manyan Labarai A Yau
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shawarci ma'aurata 1,500 da ke shirin yin auren gata na 2026 da su gina zamansu kan amana, haƙuri da tsoron Allah.
Kungiyar Jamaatu Izalatil Bidi'a Wa'iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta shirya wani babban katafaren taro tare da hadin gwiwar kungiyar Muslim World League.
Masana'antar shirya fina-finai ta Najeriya ta shiga jimami bayan rasuwar fitaccen darakta kuma mai shirya fina-finai, Dimbo Atiya, wanda ya yi fice a Nollywood.
Marubucin Najeriya Jerry Falade ya rasa kwangilar buga littafi ta sama da N2.7 biliyan bayan zargin amfani da AI wajen rubuta littafinsa, amma ya musanta zargin.
Shahararren dan Tiktok, VeryDarkMan ya bayyana sharuddan da ya ce dole a cika kafin ya amsa gayyatar 'yan sanda kan zarge-zargen da ya yi wa AIG Moshood Jimoh.
Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya bayyana dalilin da ya sa 'yan Najeriya ba su fara jin cikakken tasirin sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Bola Tinubu ba.
Bincike ya nuna cewa wani dillalin motoci ya shaida wa masu bincike yadda ake zargin Kanal Mohammed Ma’aji ya sayi motoci shida kan N65m yayin shirin juyin mulki.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta bayyana cewa a halin yanzu tana gudanar da bincike kan jihohi kusan 18 bisa zargin almundahanar kuɗaɗen gwamnati.
Mijin tsohuwar Ministar Kuɗi, Kemi Adeosun, Anthony Adeosun, ya rasu yana da shekara 62 a duniya, kamar yadda iyalansa suka sanar a cikin wata sanarwa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari