Yan APC Sun Samu Raunuka bayan Yan Daba Sun Tarwatsa Kamfen APC da Harbe Harbe
- Rikici ya barke a Ilesa, Osun, yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan gangamin yakin neman zaben gwamnan APC
- Wani jigo a APC ya zargi ɗan majalisar jihar Olawale Akerele da jagorantar waɗanda suka kai harin, tare da neman a kama shi
- Sai dai Akerele ya musanta zargin, yana cewa jami’an tsaron Amotekun da ke tare da shi ne suka harba bindiga sama domin kare kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilesa, Osun - An shiga cikin tashin hankali a Ilesa, Osun bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan gangamin yakin neman zaben gwamnan jam’iyyar APC.
Rahotanni sun ce magoya bayan APC sun gudanar da gangamin a yankin Oke-Omiru na Ilesa, inda suka nufi Isokun lokacin da lamarin ya faru.

Source: Original
Yan daba sun farmaki yan APC
Wani ɗan jam’iyyar mai suna Segun ya ce suna gudanar da gangamin ne lokacin da wasu ‘yan daba suka yi musu kwanton bauna, waɗanda ake zargin wani ɗan majalisar dokokin Osun ne ya jagoranta, cewar The Nation.
Ya ce:
“Muna gudanar da gangamin da sanyin safiyar yau, lokacin da muke komawa sakatariyarmu. ‘Yan daba suka yi mana kwanton bauna, waɗanda wani ɗan majalisar dokokin Osun ke jagoranta.
“‘Yan daban sun harba bindiga sama domin tsoratar da mu, amma wasu daga cikinmu suka tsaya. Sai muka tunkare su, sannan suka fara harbin cikin gangamin, lamarin da ya jikkata mambobi da dama.”
Wani jami’in APC ya bayyana cewa an kai wasu daga cikin mambobin da suka samu raunuka asibiti. Ya ce harsashi ya sami direban wata mota da kuma wasu masu wucewa.
Ya kuma bayyana cewa ɗaya daga cikin mambobin jam’iyyar mai suna Tobi yana samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Wesley Guild.
Shugaban yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC, Oluremi Omowaiye, ya zargi ɗan majalisar Accord, Olawale Akerele, da hannu wajen kai harin.

Source: Instagram
Yan APC sun yi zanga-zanga a Osun
Bayan harin, wasu mambobin APC a Ilesa sun gudanar da zanga-zanga a kan tituna, inda suka bukaci a kama Akerele, wanda shi ne Babban Mai Tsawatarwa na Majalisar Dokokin Osun.
Da yake mayar da martani, Akerele ya ce yana tuki ne a kan titin Isokun lokacin da gangamin APC ya haɗu da shi, cewar Punch.
Ya ce:
“Sun fara harba bindiga sama, amma jami’an tsaro na Amotekun suna cikin motata. Su ma suka harba bindiga sama domin tsoratar da su. Daga nan muka bar wurin."
Lamarin ya ƙara jawo damuwa a lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaɓen gwamnan Osun na 2026, yayin da ake kira ga jam’iyyun siyasa da magoya bayansu su guji tashin hankali.
Yan daba sun yiwa dan APC jina-jina
A baya, an ji cewa taron zaɓen unguwanni na jam’iyyar APC da ke gudana a jihar Ondo ya rikide zuwa tashin hankali, inda mutane biyu suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata.
Lamarin ya faru ne kasa da awa 24 bayan wasu ’yan daba sun kai hari sakatariyar APC da ke Akure, inda suka tarwatsa taron masu ruwa da tsaki da ake tsaka da yi.
Rahotanni sun nuna nuna cewa a yayin harin, an kai wa shugabanni farmaki da sauran jagororin jam’iyyar a jihar, tare da jikkata wasu mambobi.
Asali: Legit.ng

