Jam'iyyar NDC Ta Su Kwankwaso Ta Yi Rashin Nasara a Kotu

Jam'iyyar NDC Ta Su Kwankwaso Ta Yi Rashin Nasara a Kotu

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da jam’iyyar NDC mai adawa a Najeriya ta shigar a gabanta
  • Kotun ta ce Sashe na 138 na Dokar Zabe ya dace da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, domin yana bayyana hanya da wa’adin shigar da korafi
  • Mai shari’a Muhammed Umar ya ce dole ne a kalubalanci cancantar dan takara tun a matakin kafin zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da jam’iyyar NDC ta shigar tana kalubalantar wasu tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026.

Jam’iyyar adawa ta kalubalanci tanade-tanaden dokar da suka shafi cancanta da rashin cancantar masu neman mukaman siyasa ta hanyar zabe.

NDC ta yi rashin nasara a kotu
Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taron NDC Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Mai shari’a Muhammed Umar ya ce karar mai lamba FHC/ABJ/CS/635/2025 ba ta da ingantaccen dalili, jaridar Daily Trust ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Tinubu na tsaka mai wuya, babban jigo ya tayar da rigima a APC kan takarar shugaban ƙasa a 2027

NDC ta kai kara kotu

NDC ta shigar da karar ne a kan Antoni Janar na Tarayya da magatakardar Majalisar Tarayya da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

An kuma shigar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) cikin karar, inda jam’iyyar ta nemi kotu ta bayyana cewa Sashe na 138 da Sashe na 77(5) na Dokar Zabe ta 2026 sun sabawa kundin tsarin mulki.

Jam’iyyar ta kuma roki kotun ta tabbatar da cewa har yanzu ana iya tada batun cancantar dan takara bayan gudanar da zabe.

Abin da kotu ta yanke

Sai dai a hukuncinsa, Mai shari’a Umar ya amince da korafe-korafen farko da aka gabatar kan ingancin karar.

Ya ce abin da NDC ta nema shi ne kotu ta fassara tanade-tanaden kundin tsarin mulki da na dokar zabe.

Alkalin ya kuma ce tanade-tanaden Dokar Zabe da ake takaddama a kansu suna cike gurbin kundin tsarin mulki ne, ba su sabawa juna ba.

Kara karanta wannan

An bayyana lokacin da Israila za ta janye sojojinta daga Gaza

Ya kara da cewa hada jadawalin zaben INEC da takardar fara shari’ar ba ya mayar da karar wata shari’ar kafin zabe.

Kotu ta soke karar magatakarda

Dangane da korafin da magatakardar Majalisar Tarayya ya gabatar, Mai shari’a Umar ya ce NDC ba ta bi tanadin doka na aika sanarwar kafin fara shari’a ba.

Ya ce rashin aika irin wannan sanarwa ga wanda ake kara na biyu ya sa karar ba ta da inganci a kansa. Saboda haka, kotun ta soke karar da aka shigar a kan magatakardar Majalisar Tarayya.

Matsayar kotu kan Sashe na 138

A kan muhimmin batun karar, alkalin ya yi watsi da hujjar NDC cewa Sashe na 138 na Dokar Zabe ya sabawa tanade-tanaden kundin tsarin mulki kan cancanta da rashin cancantar masu neman mukaman siyasa.

Mai shari’a Umar ya ce kundin tsarin mulki ne ya kayyade sharuddan cancanta da rashin cancanta ga mukaman da ake zaba.

Sai dai Dokar Zabe tana bayyana hanya da wa’adin gabatar da korafe-korafen da suka taso daga zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasa.

Kara karanta wannan

Ba Atiku ba Obi ba: 'Dan takarar shugaban kasa da ya cancanci 'yan adawa su tsaida a 2027

Ya kara da cewa idan aka karanta Sashe na 138 tare da sauran tanade-tanaden Dokar Zabe, ba ya sabawa kundin tsarin mulki.

Kotu ta yi watsi da karar NDC
Taswirar birnin tarayya Abuja Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kotu ta tsaya kan hukuncin baya

Mai shari’a Umar ya kuma ki soke Sashe na 77(5) na Dokar Zabe. Ya ce Kotun Daukaka Kara ta riga ta yanke hukunci kan wannan batu a wata shari’a da ta gabata.

A cewarsa, kotun daukaka kara ta riga ta bayyana matsayarta kan tanadin, wanda ke nufin cewa kotuna gaba daya suna da alhakin bin hukuncin da kotu ta yanke a baya.

Sanata Hanga ya fice daga NDC

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Rufai Hanga, ya fice daga jam'iyyar NDC.

Murabus din Sanata Hanga na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun sauya alakar siyasa gabanin zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng