Kano: Gwamna Abba Ya Kaddamar da Aikin da ba a Taba Ganin Irinsa ba a Arewacin Najeriya

Kano: Gwamna Abba Ya Kaddamar da Aikin da ba a Taba Ganin Irinsa ba a Arewacin Najeriya

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da hedikwatar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC)
  • Abba Gids Gids ya kuma bude sabuwar cibiyar kula da masu cutar sikila ta Abba Care, wadda ita ce irinta ta farko a Arewacin Najeriya
  • Gwamnatin jihar ta fara rabon na’urorin zamani 3,000 na auna hawan jini ga manyan ma’aikata da masu rike da mukaman siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da hedikwatar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC).

Haka zalika Gwamna Abba ya kuma bude cibiyar kula da masu cutar sikila ta Abba Care da ke Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, irinta ta farko a fadin Arewacin Najeriya.

Abba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da cibiyar kula da masu ciwon sikila Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yanke hukunci, ya yi wa shugaba Tinubu alkawarin 95% na kuri'u a zaben 2027

Gwamnan ya bayyana ayyukan a matsayin manyan matakai da ke nuna kudirin gwamnatinsa na kara inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.

A yayin bikin, Abba ya kuma kaddamar da rabon na’urorin zamani 3,000 na auna hawan jini ga manyan ma’aikatan gwamnati da masu rike da mukaman siyasa.

Hakazalika, an fara rabon kayan kula da lafiyar mata masu juna biyu da jarirai, kayan aikin sashen gaggawa da kuma zanin gado guda 4,855 ga cibiyoyin kiwon lafiya na mataki na biyu a fadin Kano.

KNCDiC za yaki barkewar cututtuka

Gwamnan ya ce sabuwar Cibiyar Kula da Cututtuka ta KNCDC, an kafa ta ne domin karfafa sa ido kan cututtuka, gudanar da gwaje-gwaje, bibiyar masu mu'amala da masu dauke da cuta, kula da marasa lafiya, da hana yaduwar cututtuka.

Ya ce:

"Yau rana ce mai tarihi ga Jihar Kano. Muna bikin manyan nasarori guda hudu da ke nuna hangen nesa, tausayi da kudirin wannan gwamnati."

Kara karanta wannan

Layi ya zo kan talakawa, gwamna zai raba Naira biliyan 4 a mazabun jiharsa

Cibiyar sikila ta farko a Kano da Arewa

Abba Yusuf ya bayyana cewa cibiyar Abba Care ita ce cibiyar kula da masu cutar sikila ta farko irinta a Jihar Kano da ma Arewacin Najeriya.

A cewarsa, cibiyar za ta rika ba da cikakken kulawa kyauta ga masu fama da cutar sikila, ciki har da gano cutar, ba da shawara, magani da ilimantar da jama'a.

Abba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf a wurin kaddamar da hedkwatar cibiyar kula da cututtuka a jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ya ce dubban iyalai a Kano na fama da matsalar sikila, yayin da yara da dama ke fuskantar matsanancin ciwo da sauran matsalolin da ka iya jefa rayuwa cikin hadari.

Abba Yusuf ya sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko ga kiwon lafiya ta hanyar kara zuba jari a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da na biyu.

Abba ya yi sababbin nade-nade a Kano

A baya, kun ji cewa gwamnatin Kano ta amince da naɗin sababbin sakatarorin dindindin 19 tare da sauya wa 14 da ke kan aiki ma’aikatu.

An sanar da sauye-sauyen ne a ranar Talata cikin wata sanarwa da Shugabar Ma’aikatan Jihar Kano, Hajiya Bilkisu Shehu-Maimota, ta fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262