Shugaban EFCC Ya Ballo Ruwa, an Bukaci Ya Yi Murabus daga Mukaminsa
- Jam'iyyar Accord ta bukaci shugaban EFCC ya yi murabus kan rufe asusun gwamnatin jihar Osun kafin zaben gwamna
- Accord ta yabawa Shugaba Bola Tinubu bisa umarnin da ya bayar na cire rufe asusun domin ci gaba da gudanar da mulki
- Jam'iyyar ta kuma yi zargin an tsare kimanin magoya bayanta 60 tare da neman a gudanar da zaben Osun cikin adalci da lumana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Abuja - Jam'iyyar Accord ta bukaci shugaban Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta'annati (EFCC) ya yi murabus nan take saboda matakin rufe asusun gwamnatin jihar Osun.
Jam'iyyar ta ce matakin ya tauye dimokuradiyya tare da jefa martabar hukumar yaki da cin hanci da rashawa cikin tabo.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce shugaban jam'iyyar na kasa, Cif Maxwell Mgbudem, ya bayyana hakan a wajen taron manema labarai a Abuja ranar Juma'a, 7 ga watan Agustan 2026
Ta kara da cewa idan shugaban EFCC bai yi murabus ba, ya kamata Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauke shi daga mukaminsa domin dawo da amincewar jama'a ga hukumar.
Accord ta yabawa Tinubu
Maxwell ya yabawa Shugaba Tinubu bisa umarnin da ya bai wa EFCC na gaggauta cire rufe asusun gwamnatin jihar Osun.
Ya zargi EFCC da wuce iyakar ikon da kundin tsarin mulki ya ba ta ta hanyar daskarar da asusun jihar gabanin zaben gwamnan Osun da za a gudanar ranar 15 ga watan Agusta.
"Ya kamata shugaban EFCC ya bi tafarkin mutunci ya gabatar da murabus dinsa. Idan ya ki yin murabus, Shugaba Tinubu ya kamata ya sallame shi nan take domin dawo da martabar hukumar yaki da cin hanci da rashawa." In ji shi
Fadar shugaban kasa ta soke umarnin
Daga baya Fadar Shugaban Kasa ta sanar da cewa Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin janye matakin daskarar da asusun.
Ta bayyana abin da ya faru a matsayin abin kunya, tare da jaddada cewa dole ne a cire daskarar domin tabbatar da ci gaba da gudanar da mulki ba tare da tangarda ba.
Accord ta nemi adalci a zaben Osun
Da take mayar da martani kan matakin shugaban kasa, Jam'iyyar Accord ta ce umarnin Tinubu ya taimaka wajen kauce wa rikicin kundin tsarin mulki.
Jam'iyyar ta bukaci hukumomin tsaro, hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da sauran cibiyoyin dimokuradiyya su kasance masu tsaka-tsaki yayin gudanar da zaben gwamnan Osun.
Har ila yau, ta yi zargin ana cin zarafi, tsoratarwa da kama mambobinta a jihar Osun. Jam'iyyar ta roki Shugaba Tinubu da Sufeto Janar na 'Yan Sanda su tabbatar da sakin kusan magoya bayanta 60 da ake zargin ana tsare da su a Abuja da jihohin Osun da Nasarawa.

Source: Original
A karshe, Accord ta bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da hukumomin tsaro su tabbatar da gudanar da zaben gwamnan Osun cikin 'yanci, adalci da lumana a ranar 15 ga watan Agusta.
Gwamna Adeleke ya kai karar EFCC

Kara karanta wannan
An yi walƙiya: ADC ta nemi Tinubu ya yi wa El Rufa'i yadda aka yi wa gwamnatin Osun
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, ya shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan Hukumar EFCC.
Gwamna Adeleke ya dauki matakin ne biyo bayan hukumar yaki da cin hancin ta rufe da asusun rabon kuɗaɗen gwamnatin jihar.
Asali: Legit.ng

