Kano Ta Sake Shiga Gaban Jihohi, Gwamna Abba Ya Samu Lambar Yabo daga NAWOJ
- Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sake samun lambar yabo kan kokarin da yake yi na kafa shigabanci nagari
- Ƙungiyar NAWOJ ta karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf da lambar yabo kan zaman lafiya, tsaro da shugabanci nagari
- An gabatar da lambar yabon ne a taron mata han jarida kan tsaro na Women In Security Summit and Awards 2026, da aka gudanar a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ƙungiyar mata yan jarida ta Najeriya (NAWOJ) ta karrama Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da lambar yabo kan zaman lafiya, tsaro da shugabanci nagari.
Bayanai sun nuna cewa an ba gwamnan lambar yabon ne saboda irin ci gaban da gwamnatin sa ke samarwa a jihar Kano daga watan Mayun 2023 zuwa yau.

Source: Facebook
Gwamna Abba ya karbi lambar yabo
Leadership ta ruwaito cewa an gudanar da bikin bayar da lambar yabon ne a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja, a matsayin wani ɓangare na taron NAWOJ kan tsaro na 2026.
Taken taron shi ne "Strategic Role of Women In Strengthening National Security Through Leadership, Innovation and Collaborative Partnership."
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya karɓi lambar yabon a madadin gwamnan.
A cikin wata sanarwa da Kwamared Waiya ya fitar, ya ce lambar yabon ta nuna amincewa da irin kyakkyawan aikin gwamnati wajen gudanar da harkokin jama'a.
NAWOJ ta yabawa gwamnatin Kano
Babban Daraktan hukumar National Blood Service Agency, Farfesa Saleh Yuguda, ne ya gabatar da lambar yabon ga Gwamna Abba Gida-Gida a madadin kungiyar NAWOJ.
Da yke jawabi bayan mika kambar yabon, Farfesa Yuguda ya ce ƙungiyar ta yi nazari kan nasarorin gwamnatin Abba Kabir Yusuf kafin ta zaɓe shi domin wannan karramawa.
Ya ce wannan yabo zai ƙara ƙarfafa sauran shugabanni su yi koyi da irin salon shugabancin gwamnan domin gina jagoranci mai nagarta, wanda jama'a za su amfana.

Source: Facebook
Kungiyar ta yaba wa Abba kan naɗa mata
Kungiyar mata yan jarida ta NAWOJ ta kuma bayyana cewa gwamnatin Kano ta nuna ƙwazo wajen tabbatar da shigar mata cikin harkokin shugabanci da yanke shawara, kamar yadda Daily Post ta kawo.
A cewar Ƙungiyar, mata na jagorantar muhimman hukumomi da cibiyoyi a jihar Kano, lamarin da ke taimakawa wajen sauya akalar ci gaban Kano da kuma ƙarfafa rawar da mata ke takawa a gwamnati.
Gwamna Abba ya kafa tarihi a Kano da Arewa
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da hedikwatar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC).
Haka zalika Gwamna Abba ya kuma bude cibiyar kula da masu cutar sikila ta Abba Care da ke Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, irinta ta farko a fadin Arewacin Najeriya.
A cewarsa, cibiyar za ta rika ba da cikakken kulawa kyauta ga masu fama da cutar sikila, ciki har da gano cutar, ba da shawara, magani da ilimantar da jama'a.
Asali: Legit.ng

