Manyan Labarai A Yau
Sabbin alkaluman DMO sun nuna bashin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 159.35 a watan Maris na 2026, bayan karin kusan Naira tiriliyan 10 cikin shekara guda.
Bayan rasa matarsa da 'ya'yansa shida a wani mummunan hari, Haruna Bashir ya sake yin aure a shirin auren gata na gwamnatin Kano da ya hada ma'aurata 1,500.
Ƙungiyar NAWOJ ta ba Gwamna Abba Kabir Yusuf lambar yabo ta zaman lafiya, tssfo da shugabsnci nagari saboda nasarorin gwamnatinsa da ƙarfafa mata a shugabanci.
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace manoma biyu a jihar Ondo, inda suka bukaci a biya Naira miliyan 100 kafin su saki manoman da suka aace.
Dan majalisar dokokin Iran, Ebrahim Rezaei, ya gargadi Saudiyya cewa yarjejeniyar tsaro da ta kulla da Pakistan da Turkiyya ba za ta tabbatar mata da tsaro ba.
Wani sabon rikici mai muni ya barke tsakanin bangarorin kungiyar Boko Haram a jihar Borno, bayan mayakan Islamic State West Africa Province (ISWAP) sun kai hari.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa an tura kudi cikin wani asusunsa na sirri daga wanda bai sani ba, lamarin da ya ce ya tayar da tambayoyi kan tsaron bayanan bankin.
Hukumar ICPC ta bayyana cewa Fadar Shugaban Kasa ba ta nada Adeniyi Adeyemi ba kuma ba ta kirkiri PFIPC ba. Hukumar ta ce takardar nadinsa jabu ce.
Atiku Abubakar ya kalubalanci Shugaba Bola Tinubu da ya umarci ICPC ta saki Nasir El-Rufai, yana mai cewa shugaban ya nuna yana da ikon ba hukumomi umarni.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari