Tura Ta kai Bango, an Bukaci Sojoji Su Yi Zuwa Daya Su Gama da 'Yan Bindiga a Kebbi

Tura Ta kai Bango, an Bukaci Sojoji Su Yi Zuwa Daya Su Gama da 'Yan Bindiga a Kebbi

  • Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya bukaci Rundunar Sojin Najeriya ta kawar da 'yan bindigan da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar
  • Gwamnan ya yi wannan kiran ne yayin wata ziyarar ba-zata da ya kai sansanin sojoji a Yauri, inda ya yaba da jajircewarsu wajen kare al'umma
  • Idris ya ce gwamnatin Kebbi za ta ci gaba da bai wa jami'an tsaro goyon bayan da suke bukata domin tabbatar da tsaro da kuma bai wa manoma damar komawa gonakinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Yauri – Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi kira ga Rundunar Sojin Najeriya da ta yi amfani da dukkan ƙarfinta wajen kawar da 'yan bindigan da ke ci gaba da barazana ga rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar.

Kara karanta wannan

2027: Babban jigon APC a Arewa ya tada rigima, ya ce ba zai sake tallata Tinubu ba

Gwamnan ya yi wannan kiran ne ranar Juma'a yayin wata ziyarar ba-zata da ya kai wa dakarun sojoji a sansaninsu da ke Yauri, inda ya yaba musu kan jajircewa da sadaukar da kansu wajen gudanar da aikinsu.

Gwamna Nasir Idris
Gwamnan jihar Kebbi a wajen taro. Hoto: Kebbi State Government
Source: Facebook

Channesl TV ta wallafa cewa Gwamna Idris ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da goyon baya da yanayin da zai bai wa jami'an tsaro damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Maganar kawar da 'yan bindiga

Gwamnan ya ce tabbatar da tsaro nauyin kowa ne, yana mai kira ga gwamnatocin jihohi da su kasance masu taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa gwamnatin tarayya wajen kare al'ummomin da ke cikin barazana.

Leadership ta rahoto ya ce hakan zai taimaka wajen samar da yanayin da manoma za su iya komawa gonakinsu cikin aminci domin gudanar da harkokin noma.

A cewarsa, 'yan bindiga na ƙoƙarin kawo wa jihar cikas ta hanyar kai hare-hare kan al'umma, don haka ya kamata jami'an tsaro su yi amfani da ƙwarewar sojojin Najeriya wajen kawar da su.

An tura ƙarin sojoji Kebbi

Gwamnan ya kuma gode wa Babban Hafsan Sojin Ƙasa bisa tura ƙarin rundunonin soji zuwa jihar domin ƙarfafa yaƙi da 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya yi maganar sulhu da 'yan bindiga bayan ya je ta'aziyya

Ya ce matakin ya cika buƙatar gwamnatin jihar na ƙara yawan jami'an tsaro a yankunan da hare-haren 'yan bindiga suka fi shafa.

“Na yi farin ciki da ayyukanku. Babban Hafsan Sojin Ƙasa, tare da goyon bayan shugabannin rundunar, ya amsa kiranmu ta hanyar turo ku nan Kebbi.
“Kasancewarku za ta ƙara ƙarfi ga ayyukan sauran hukumomin tsaro,”

In ji gwamnan.

Ya bayyana yankin Yauri, Shanga da Ngaski a matsayin wani yanki da ke fuskantar kutsen 'yan bindiga daga jihohin Neja, Zamfara da Kwara.

Gwamnan ya ce kafin isowar ƙarin sojojin, sauran hukumomin tsaro suna gudanar da ayyukansu, amma zuwan sababbin dakarun zai ƙara musu ƙwarin gwiwa.

Taswirar jihar Kebbi
Taswirar jihar Kebbi a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Kafin ziyarar sansanin sojojin, Gwamna Idris ya kai gaisuwar ban girma ga Sarkin Yauri, Dakta Muhammad Zayyanu Abdullahi, a fadarsa.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda 69

A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar Sojin Najeriya ta kashe 'yan ta'adda 69 tare da ceto sama da mutane 360 da aka yi garkuwa da su cikin mako guda.

Daraktan Ayyukan Yaɗa Labaran Tsaro na DHQ, Manjo Janar Michael Onoja, ya ce an kuma kama mutane 49 da ake zargi da aikata laifi a yayin ayyukan sojojin.

Onoja ya ce nasarorin sun samu ne sakamakon ci gaba da kai hare-haren ƙasa, sama da ruwa kan masu aikata laifi a sassa daban-daban na ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng