Mutumin da Ya Rasa Matarsa da 'Ya'Yansa 6 a Kano Ya Sake Sabon Aure
- Haruna Bashir da ya rasa matarsa da 'ya'yansa shida bayan an yi masu kisan gilla ya sake yin aure
- Gwamnatin Kano ta biya sadaki, ta ba shi tallafi tare da kai shi Umrah, aikin Hajji da kuma ba shi gida
- An daura auren mutane 1,500 a fadin kananan hukumomi 44 domin tallafa wa zawarawa da sauran masu bukata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Jihar Kano – Haruna Bashir, mutumin da ya rasa matarsa da 'ya'yansa shida bayan an kashe su a farkon shekarar nan, ya sake yin aure a karkashin shirin auren gata da gwamnatin jihar Kano ta shirya wa ma'aurata 1,500.
An daura auren Bashir ne ranar Juma'a a Babban Masallacin Juma'a da ke Fadar Mai Martaba Sarkin Kano.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa ya auri Nabila Kabiru Yunusa, inda aka biya sadakin N200,000 a madadinsa.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ne ya wakilci ango a matsayin waliyyi, yayin da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya wakilci amaren.
Haruna Bashir ya rasa iyalansa shida
A ranar 17 ga Janairu, 2026, wasu mahara sun kai hari gidan Haruna Bashir da ke unguwar Dorayi Chiranchi a Kano.
Maharan sun kashe matarsa, Fatima Abubakar, tare da 'ya'yansu shida, lamarin da ya jefa Bashir cikin babban rashi.
Gwamnatin Kano ta ba Bashir karin tallafi
Da yake jawabi yayin bikin, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa, ya ce gwamnatin jihar ta kara ba Bashir tallafi domin taimaka masa ya farfado daga wannan mummunan ibtila'i.
Ya bayyana cewa gwamnatin ta dauki nauyin tafiyarsa zuwa Umrah, ta saukaka masa gudanar da aikin Hajji, sannan ta ba shi gida a Amana City domin rage masa radadin halin da ya shiga.
An daura auren mutane 1,500
An gudanar da shirin auren gatan ne lokaci guda a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar Kano. Shirin ya kasance wani bangare na kokarin gwamnatin jihar na tallafa wa zawarawa da sauran wadanda suka cancanta.
A karkashin wannan tsari, kowace amarya ta samu sadakin N200,000, tare da karin tallafin kudi domin fara karamar sana'a.
An shawarci ma'aurata su zauna lafiya
Sheikh Aminu Daurawa ya bukaci sababbin ma'auratan su kiyaye darajar aure, su zauna cikin zaman lafiya tare da gina iyalai nagari da za su amfani al'umma.
Shi ma Babban Limamin Jihar Kano, Farfesa Sani Zahraddeen, wanda ya jagoranci daurin auren, ya shawarci ma'auratan da su rika mu'amala da juna cikin kauna, adalci da kyautatawa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Ya kuma tunatar da maza, musamman masu mata fiye da daya, cewa adalci wajibi ne a tsakanin matansu.

Source: Facebook
Gwamna Abba ya samu lambar yabo
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar mata yan jarida ta Najeriya (NAWOJ) ta karrama Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da lambar yabo kan zaman lafiya, tsaro da shugabanci nagari.
An ba gwamnan lambar yabon ne saboda irin ci gaban da gwamnatin sa ke samarwa a jihar Kano daga watan Mayun 2023.
Asali: Legit.ng

