Trump ya gama barazana ya fadi lokacin kawo karshen yaki da Iran

Trump ya gama barazana ya fadi lokacin kawo karshen yaki da Iran

  • Shugaba Donald Trump ya yi magana kan yakin da Amurka ke yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran wanda ya dauki dogon lokaci
  • Iran na ci gaba da tattaunawa da Oman kan hanyar zirga-zirga ta mashigar Hormuz, amma ta ce ba ta tattaunawa kai tsaye da Amurka
  • Masanin siyasa Robert Pape ya yi gargadin cewa rikicin na iya ɗaukar lokaci saboda halin da Amurka ta tsinci kanta a ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Donald Trump, shugaban ƙasar Amurka, ya yi magana kan lokacin da yake ganin za a kawo karshen yaki da Iran.

Shugaba Trump ya bayyana cewa yana ganin yakin da ake yi da Iran zai ƙare "nan ba da jimawa ba."

Trump ya yi magana kan yaki da Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yaushe yaki da Iran zai kare?

Tashar Aljazeera ta ce Trump ya yi wannan bayani ne yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida game da farashin makamashi a Amurka da kuma kasuwannin duniya.

Kara karanta wannan

Trump ya fusata, ya yi ƙarin haske kan jita jitar cewa suna fama da ƙarancin makamai

"Ba na tunanin za su iya ci gaba da wannan na dogon lokaci." In ji shi

Iran na tattaunawa da Oman

A halin yanzu, Iran na tattaunawa da ƙasar Oman domin cimma yarjejeniya kan yadda jiragen ruwa za su rika wucewa ta mashigar Hormuz cikin tsarin da bangarorin biyu za su amince da shi.

Ana sa ran hakan zai ƙara yawan zirga-zirgar jiragen ruwa na kasuwanci ta wannan muhimmin mashigin ruwa.

Sai dai Iran ta sake jaddada cewa ba ta shiga wata tattaunawa kai tsaye da Amurka ba domin cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yakin har abada.

Trump ya musanta ƙarancin makamai

Trump ya kuma ƙaryata rahotannin da ke cewa Amurka na fuskantar ƙarancin makamai.

"Muna da makamai marasa iyaka. Muna cikin kyakkyawan matsayi. Muna da dumbin alburusai." In ji shi.

Fadar White House da ma'aikatar tsaron Amurka (Pentagon) sun sha musanta rahotannin da ke cewa adadin makaman kai hari da na kariya sun ragu zuwa matakin da ke haddasa damuwa.

Kara karanta wannan

Iran ta gindaya sharadin bude mashigar Hormuz da Trump ke son ta yi

A baya, Trump ya yi alƙawarin gano mutanen da suka fitar da bayanan sirri bayan waɗannan rahotanni sun bayyana.

Masani ya yi hasashen rikicin ba zai ƙare nan kusa ba

Robert Pape, farfesa a fannin kimiyyar siyasa a Jami'ar Chicago, ya ce ba ya ganin yakin Amurka da Iran zai samu mafita ta dindindin cikin gaggawa.

A cewarsa, Trump ya tsinci kansa cikin wani yanayi mai wahalar fita.

Pape ya shaida wa Al Jazeera cewa:

"Muna cikin mafi muni irin tarkon ƙara ta'azzara rikici a tarihi."

Ya ƙara da cewa:

"Ko dai Shugaba Trump ya ja da baya ya bar Iran ta ci gaba da ƙarfafa matsayinta har ta zama babbar ƙasa mai tasiri a Tekun Fasha, mai yiwuwa ma ta mallaki makamin nukiliya nan gaba, ko kuma ya ƙara tsananta rikicin. A ganina, babu wata hanya ta uku."
Trump ya ce za a kawo karshen yaki da Iran
Shugaba Donald Trump na Amurka a Oval Ofis Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya rattaba hannu kan dokoki

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanya hannu kan dokokin zartarwa guda biyu kan samun zama dan kasa.

Trump ya sanya hannu kan dokokin ne da nufin takaita samun zama ɗan ƙasar Amurka ta hanyar haihuwa a wasu yanayi tare da ƙara tsaurara matakan gwamnatin tarayya kan abin da ake kira 'yawon zuwa haihuwa'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng