Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin Kano ta kashe sama da Naira biliyan 1.5 wajen shirin Auren Gata na 2026, inda ma’aurata 1,500 suka samu tallafin aure da na fara rayuwar gida.
X ya sanar da dakatar da shirin rabon kudaden shiga ga masu ƙirƙira daga Satumba 2026 tare da ƙaddamar da sabon shirin lada ga masu wallafa abun ciki na asali.
Rundunar ’yan sandan jihar Osun ta kama Kwamishinan Muhalli da Tsaftar Muhalli na jihar, Mayowa Adejoorin, bisa zargin da ya shafi harbe-harbe da ya faru.
Samuel Ortom ya karyata rahoton cewa shugabannin PDP na jihar Benue na shirin sauya ɗan takarar gwamna na jam’iyyar, Samuel Aondoakaa a zaɓen 2027.
Hunter Biden ya ce ciwon dajin da mahaifinsa, Joe Biden ke fama da shi ya bazu zuwa ƙasusuwansa, yana haifar masa da ciwo da raunana jikinsa gaba daya.
Jorge Messi, mahaifin Lionel Messi kuma wakilinsa na dogon lokaci, ya rasu yana da shekaru 68 bayan fama da rashin lafiya na tsawon lokaci a Argentina.
Shugaba Bola Tinubu ya yi jimamin rasuwar babban limamim coci, Emmanuel Abiodun Alogbo, shugaban darikar Cherubim and Seraphim, tare da yabawa gudunmawarsa.
An bayyana cewa yara 25 daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a Kebbi, Kwara da Neja sun mutu a hannun 'yan ta'adda yayin da suke tsare a hannunsu.
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya samu lambar yabo ta ZIK International Peace and Leadership Award a Ghana kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari