Gwamna a Arewa Zai Mayar wa Alhazan Jiharsa kusan Naira 55,000 bayan Hajjin 2026

Gwamna a Arewa Zai Mayar wa Alhazan Jiharsa kusan Naira 55,000 bayan Hajjin 2026

  • Gwamnatin Jigawa ta amince da mayar wa kowane maniyyacin jihar da ya yi Hajjin 2026 N53,853, wato kusan N55,000, daga kuɗaɗen da suka yi saura
  • Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jigawa ta mayar da N44.9m na kuɗin Hajji da suka yi saura ga gwamnatin jihar
  • Sarkin Dutse ya buƙaci gwamnatin jihar ta gina sansanin wucin gadi na dindindin domin maniyyata kafin tafiya Hajji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza Daudawa ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Jigawa – Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da mayar wa kowane maniyyacin jihar da ya gudanar da aikin Hajjin 2026 N53,853, wato kusan N55,000, bayan dawowar wasu kuɗaɗen da suka yi saura daga aikin Hajjin.

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar ce ta mayar da kuɗaɗen da suka yi saura ga gwamnatin jihar bayan kammala aikin Hajjin bana.

Kara karanta wannan

"Na ji kunya": Tinubu ya ba EFCC umarnin bude asusun gwamnatin Osun da aka rufe

Gwamnatin Jigawa za ta mayarwa alhazai rarar kudin aikin Hajjin 20026
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi. Hoto: @uanamadi
Source: Twitter

Jigawa: An mayar da rarar kudin Hajji

Sakataren zartarwa na hukumar, Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ranar Juma’a yayin da yake gabatar da rahoton kwamitin Hajjin 2026 ga Gwamna Umar Namadi a gidan gwamnatin jihar da ke Dutse, in ji rahoton Punch.

Ya ce hukumar ta mayar da N44.9m na kuɗaɗen Hajji da suka yi saura ga gwamnatin jihar.

“Daga cikin wannan kuɗi, gwamnati ta amince da N53,853, kusan N55,000, a mayar wa kowane maniyyacin da ya gudanar da Hajjin bana,” in ji Labbo.

Sakataren zartarwar ya ƙara da cewa hukumar ta kuma mayar da wasu N27.2m zuwa baitulmalin gwamnatin jihar a matsayin ƙarin kuɗaɗen da ba a kashe ba yayin gudanar da aikin Hajjin 2026.

Ya bayyana aikin Hajjin bana a matsayin mafi nasara a tarihin jihar Jigawa, musamman duba da yadda aka gudanar da hidimomin da suka shafi maniyyata.

Kwamitin Hajjin 2026, wanda Sarkin Dutse, Alhaji Hameem Nuhu, ya jagoranta, ya samu yabo kan yadda ya gudanar da aikin.

Kara karanta wannan

Cikin gwamnoni 18 ya duri ruwa da EFCC ta fara bincike kan zargin karkatar da kudade

Labbo ya ce:

“Aikin Hajjin 2026 ya kasance na musamman kuma ya zarce dukkan ayyukan Hajji da jihar ta gudanar a baya.”

An samar da ayyukan kula da ido

Sakataren zartarwar ya kuma yaba wa kwamitin bisa samar da ayyukan kula da lafiyar ido ga maniyyatan Jigawa yayin da suke Saudiyya.

Ya ce wannan shiri da aka samar ƙarƙashin jagorancin Sarkin Dutse babban ci gaba ne ga jin daɗin maniyyatan jihar.

Labbo ya kuma gode wa gwamnatin jihar bisa tallafin kuɗin da ta bayar domin gudanar da aikin Hajjin.

Ya ce gwamnatin jihar ta bayar da rancen N3.4bn wanda ya taimaka wa hukumar wajen samun damar gudanar da aikin Hajjin 2026 yadda ya kamata.

Ya kuma yaba wa malaman addini da jami’an cibiyoyin kananan hukumomi bisa gudummawar da suka bayar wajen ganin an samu nasarar aikin a matakin ƙananan hukumomi.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa an sauke maniyyata a wuraren masauki da ke kusa da Masallacin Harami a Makkah tare da samar musu da abinci mai inganci a tsawon lokacin zamansu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fitar da N3.5bn, zai ba alhazan jiharsa rancen kudin zuwa aikin Hajji

Sarkin Dutse ya nemi sansanin alhazai

A nasa jawabin, Sarkin Dutse, Alhaji Hameem Nuhu, ya buƙaci gwamnatin Jigawa ta gina sansanin wucin gadi na dindindin domin maniyyatan jihar.

Ya ce bai kamata jihar ta ci gaba da dogaro da sansanin horas da matasan NYSC ba wajen shirye-shiryen aikin Hajji, saboda a wasu lokuta ana buƙatar wurin domin ayyukan ’yan bautar ƙasa.

“Ina kira ga gwamnatin jihar da ta kafa sansanin wucin gadi na dindindin na Hukumar Jin Daɗin Alhazai maimakon ci gaba da dogaro da sansanin horas da NYSC,” in ji Sarkin.
An roki gwamnatin Jigawa ta samar da sansanin alhazai na dindindin
Taswirar jihar Jigawa, inda gwamnati za ta mayar wa alhazai rarar kudin Hajjin 2026. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Namadi ya yaba da kwamitin Hajji

Gwamna Umar Namadi, yayin da yake mayar da martani bayan karɓar rahoton, ya yaba wa kwamitin bisa irin aikin da ya gudanar.

Ya musamman yabawa Sarkin Dutse bisa jagoranci da ƙoƙarin da ya nuna wajen ganin an samu nasarar aikin Hajjin 2026.

Gwamnan ya bayyana Sarkin Dutse a matsayin jagora abin koyi, yana mai cewa Jigawa ta kafa sabon tarihi wajen kula da jin daɗin maniyyata.

Kara karanta wannan

EFCC ta rufe asusun gwamnatin jiha sukutum, an jefa gwamna a matsala dab da zabe

Namadi ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar, ta hannun Hukumar Jin Daɗin Alhazai, za ta mayar wa kowane maniyyacin Jigawa N55,000 a matsayin kuɗin da ya yi saura daga kuɗin aikin Hajjin 2026.

Gwamna zai ba alhazai rancen kudi

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Jigawa ta amince da bayar da rancen Naira biliyan 3.5 ga Hukumar Jin Daɗin Alhazai domin biyan kuɗin ajiyar Hajjin 2027 ga maniyyata.

Kuɗin rancen zai taimaka wa maniyyata 466 daga jihar tare da bai wa Jigawa damar cika wa'adin da Hukumar Alhazai ta Kasa ta gindaya.

Gwamnati ta ce biyan kuɗin da wuri zai sauƙaƙa shirye-shiryen masauki, sufuri, abinci da sauran hidimomin aikin Hajjin shekarar 2027 cikin nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com