Manyan Labarai A Yau
Matawalle ya ce zaɓen 2027 zai kasance cikin gaskiya da adalci, yayin da ƙungiyar Tinubu Again Movement ke shirin ƙara yaɗa goyon bayan Bola Tinubu.
Manyan ‘yan siyasar Katsina biyu, Mustapha Muhammad Inuwa da Lawal Musa Daura, sun fice daga ADC bayan rashin nasarar samun tikitin takarar gwamna.
Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Wakilai, Abdussamad Dasuki, ya bukaci hukumar zabe ta INEC ta gudanar da zaɓen shekarar 2027 a rana guda.
Shugaban NRS, Zacch Adedeji, ya ce cire tallafin mai ya taimaka wa tattalin arzikin Najeriya, yana mai cewa kudin tallafin zai iya kai N53 tiriliyan.
Atiku Abubakar ya zargi Olusegun Obasanjo da ci gaba da yada zarge-zarge da yaudara a kansa, yana mai cewa sabbin ikirarin tsohon shugaban ƙasar ba su da tushe.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kashe wani da ake zargi da jagorantar kungiyar masu aikata laifuka a Imo, wanda ake alakanta shi da kisan wani basarake da wasu.
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ce ta kashe mayakan kungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) guda tara, ciki har da wani babban kwamandan kungiyar.
Tsohon Minista kuma jakadan Najeriya a kasar South Africa, Femi Fani Kayode, ya yi wa Sheikh Sani Yahaya Jingir, martani kan yadda ya tallata muslim-muslim.
Jonah Jang ya bayyana cewa rikicin Plateau ya samo asali ne daga matsalolin tarihi, ƙasa, adalci da shugabanci, yana mai zayyano hanyoyin kawo ƙarshen rikicin.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari