Mustapha Rabiu: Yaron Kwankwaso Ya Samu Takarar Mataimakin Gwamnan NDC a Kano

Mustapha Rabiu: Yaron Kwankwaso Ya Samu Takarar Mataimakin Gwamnan NDC a Kano

  • Jam'iyyar NDC da dan takararta na gwamna a jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, sun sanar da wanda zai yi takarar mataimakin gwamna a 2027
  • An bayyana Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin abokin takarar Aminu Abdulsalam Gwarzo a zaben 2027 da ake tunkara
  • Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso ya kasance haifaffen da ne ga madugun Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Ɗan takarar gwamna na jam'iyyar NDC a jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya zaɓi abokin takararsa a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Aminu Abdulsalam Gwarzo ya zabi Mustapha Rabiu Kwankwaso, ɗan cikin tsohon gwamnan Kano kuma madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin abokin takararsa.

Mustapha Kwankwaso ya samu tikitin takara a Kano
Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso tare da Aminu Abdulsalam Gwarzo Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce mai magana da yawun ƙungiyar Kwankwasiyya, Habibu Saleh Mohammed, ya tabbatar da wannan lamari a cikin wata gajerar sanarwa ranar Litinin, 15 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Amaechi: Jam'iyyar ADC ta sanar da abokin takarar Atiku a zaben 2027

'Dan Rabiu Kwankwaso ya samu takara

“Mai Girma Aminu Abdussalam Gwarzo ya bayyana Hon Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin abokin takararsa na zaɓen Gwamna na shekarar 2027."

- Habibu Saleh Mohammed

Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso shi ne tsohon kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano, wanda ya yi murabus daga mukaminsa.

Mustapha Kwankwaso ya samu tikiti a NDC

Hakazalika, Mai magana da yawun bakin Aminu Abdulsalam Gwarzo, Ibrahim Garba Shuaibu, ya sanar da zabin da aka yi wa Mustapha Kwankwaso a cikin sanarwa wadda Abdullahi Ghali Basaf ya sanya a Facebook.

A cikin sanarwar, an bayyana cewa an gabatar da Mustapha Kwankwaso a gaban kwamitin amintattu na jam'iyyar da kuma manyan masu ruwa da tsaki a lokacin taron tuntuɓar juna da aka gudanar a gidan Kwankwaso da ke Kano.

An bayyana zaɓen Hon. Mustapha Kwankwaso a matsayin wata dabara da yanke shawara mai kyau da nufin ƙarfafa hangen nesan jam'iyyar na samar da shugabanci na bai ɗaya, ƙarfafa matasa, ci gaban tattalin arziki a faɗin Jihar Kano.

Kara karanta wannan

2027: Tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya gana da jagororin tafiyar Obi da Kwankwaso

A cewar sanarwar, Hon. Kwankwaso ya bayyana a matsayin zaɓin da jam'iyyar ta fi so bayan tuntuɓar juna da kuma nazari tsaf da aka yi wa mutane da dama da suka cancanta.

NDC ta ba Mustapha Rabiu tikitin takara a Kano
Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso zaune a ofis Hoto: Mustapha Rabiu Kwankwaso
Source: Facebook

Me Gwarzo ya ce kan zabar Mustapha?

Yayin da yake magana kan wannan cigaba, Kwamared Gwarzo ya nuna kwarin gwiwa kan juriya da ƙarfin gwiwar abokin takararsa na bayar da gagarumin gudunmawa ga ajandar gwamnatin.

Ya lura cewa gogewarsa, kyakkyawar siffar shugabancinsa, da kuma farin jininsa a tsakanin talakawa sun sa ya zama babban jigo ga tikitin.

Sanarwar ta ƙara da cewa, jam'iyyar NDC ta yi amanna cewa tikitin Gwarzo da Kwankwaso yana wakiltar haɗakar ƙwarewa, gogewa, gaskiya, da kuma sadaukarwa da ake buƙata domin tunkarar ƙalubalen da ke fuskantar jihar Kano da kuma samar da shugabanci na gari ga al'ummarta.

Hadimin Abba ya yi zargi kan Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimin Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya yi zarge-zarge kan Rabiu Musa Kwankwaso.

Sanusi ya yi zargin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana yi wa sauran 'yan siyasa wayau, inda yake raba kafa tsakanin jam'iyyu.

Hakazalika, hadimin na gwamnan Kano ya bayyana cewa Kwankwaso ya ci amanar kansa ta hanyar ficewa daga jam'iyyar NNPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng